Siyasa Ta Dauki Zafi: Kakakin Majalisa da Ciyamomi 17 Sun Fice daga PDP zuwa APC

Siyasa Ta Dauki Zafi: Kakakin Majalisa da Ciyamomi 17 Sun Fice daga PDP zuwa APC

  • Shugaban majalisar dokokin Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya jagoranci ciyamomi 17 da wasu fitattun mambobin PDP zuwa APC
  • Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Bashiru, ya karɓi masu sauya shekar, ya ba su tabbacin cewa za su samu kyakkyawar kulawa a jam'iyyar
  • Gwamna Monday Okpebholo ya yi maraba da shugaban majalisar zuwa APC, inda ya ce hakan zai sa jihar Edo ta samu ci gaba cikin gaggawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.

An ce Agbebaku ya jagoranci shugabannin kananan hukumomi 17, da ɗimbin kansiloli, da kuma fitattun mambobin jam’iyyar PDP zuwa APC.

Shugaban majalisar jihar Edo, ciyamomi 17 da kusoshin PDP sun koma APC
Shugaban majalisar Edo, Blessing Agbebaku, Adams Oshiomhole, Gwamna Monday Okpebholo. Hoto: @Harmless47
Asali: Twitter

Kakakin majalisa da ciyamomi sun koma APC

Shugaban majalisar ya ce sun dauki wannan matakin ne domin haɗa kai da Gwamna Monday Okpebholo don hanzarta kawo ci gaba a jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, shi ne ya karɓi masu sauya shekar a madadin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sanata Ajibola ya ba su tabbacin samun daidaito a cikin APC, yana mai cewa sauya shekarsu za ta kawo gagarumin ci gaba ga ƙarfafa jam’iyyar a Edo.

Jiga jigan PDP da suka koma APC a Edo

Daga cikin waɗanda suka sauya shekar tare da kakakin majalisar akwai Hon. Sunny Ifada; Hon. Yekini Idiaye, tsohon mataimakin shugaban majalisa.

Sauran sun hada da: Hon. Roland Asoro, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisa; Hon. Nosa Nosayaba, da tsohon sakataren PDP na jihar, Gabriel Oloruntoba da sauransu.

Gwamna Okpebholo ya yi maraba da masu sauya shekar zuwa APC, inda ya yi alkawarin samar da ci gaba a Edo musamman da suka samu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Gwamnan ya bayyana cewa Edo na ganin ci gaba da ba a taɓa ganin irinsa ba saboda jihar ta samu shugaban ƙasa da ya yarda da mutanenta.

Oshiomhole ya yi maraba da masu shigowa APC

Sanata Bashiru, wanda ya yi magana a madadin Ganduje, ya yabawa Gwamna Okpebholo bisa jagorancinsa, musamman wajen tabbatar da biyan albashi a kai-a kai da kuma gyaran ababen more rayuwa kamar ayyukan hanyoyi da ake yi a Ekpoma.

Ya bayyana cewa wannan sauya shekar ta nuna gagarumin sauyin yanayin siyasa da aka samu a jihar da kuma karuwar yarda da ake yi da gwamnatin APC.

Gwamnan Edo ya yi wa wadanda suka sauya sheka maraba zuwa APC
Shugaban majalisar Edo, Blessing Agbebaku, Adams Oshiomhole, Gwamna Monday Okpebholo. Hoto: @Harmless47
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya yi maraba da komawar shugaban majalisar zuwa APC.

Oshiomhole ya ce Agbebaku ya dawo gida ne domin shi ma daya ne daga cikin waɗanda suka gina jam’iyyar a jihar tun farko.

Kakaki da 'yan majalisa 21 sun koma APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar dokokin Delta, Emomotimi Guwor, da 'yan majalisa 21 sun sanar da komawarsu APC a hukumance a ranar Talata, 6 ga Mayu.

A wasikun da suka gabatar wa majalisa, kakakin majalisar da 'yan majalisar 21 sun tabbatar da ficewarsu daga PDP zuwa APC.

Guwor ya bayyana cewa sun sauya sheka ne saboda rikicin shugabanci da ya hana PDP samun kwanciyar hankali a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.