Gwamna Ya Fayyace Dalilin 'Yan Adawa na Yin Tururuwa zuwa Jam'iyyar APC

Gwamna Ya Fayyace Dalilin 'Yan Adawa na Yin Tururuwa zuwa Jam'iyyar APC

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa APC ba ta da burin maida Najeriya ƙasa ƙarƙashin jam'iyya ɗaya
  • Abdullahi Sule ya nuna cewa abin da APC ke so shi ne ta samu rinjayen da za ta riƙa lashe mafi yawan ƙuri'u a lokacin zaɓe
  • Gwamnan Nasarawa ya kuma taɓo batun dalilin da ya sanya ƴan siyasa na jam'iyyun adawa suke komawa APC kwanan nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan tururuwar shigowar ƴan adawa zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna Sule ya bayyana cewa rinjayen da APC ke samu ba yana nufin cewa Najeriya za ta koma ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba ne.

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya ce nasarorin Tinubu ke jawo 'yan adawa zuwa APC Hoto: Abdullahi A. Sule, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Talata bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce samun rinjayen da APC ke yi ba yana nufin cewa sauran jam’iyyu sun mutu ba ne ko kuma ba su da tasiri a ƙasar nan, rahoton Tribune ya tabbatar.

Meyasa ƴan adawa ke komawa APC?

Ya ce manufofi da nasarorin Shugaba Tinubu ne suka sa ƴan siyasa na wasu jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC.

Ya bayyana cewa ba a tilastawa waɗanda suka sauya sheƙar shiga jam’iyyar ba, sai dai sauye-sauyen da Tinubu ya kawo ne suka ja ra’ayinsu.

"Wannan alama ce ta yadda jam’iyyarmu ke aiki da kuma yadda shugaban ƙasa ke gudanar da mulki.”
“Mun ga gyare-gyare a ɓangaren daidaita farashin canji, cire tallafin mai, da kuma yanzu a ɓangaren wutar lantarki."
“Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda aka mayar da hankali wajen koyar da sana’o’i da kuma harkar noma. Waɗannan gyare-gyare ne da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya ce Najeriya ba za ta koma kasa mai jam'iyya 1 ba Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Me jam'iyyar APC ke son samu a Najeriya?

Ya ƙara da cewa a tsarin dimokuraɗiyya, kowace jam’iyya na da burin ta fi sauran rinjaye da samun nasara a zaɓe, ko da kuwa akwai sauran jam’iyyu.

Gwamnan ya kawo misalin jam’iyyun Republican da Democratic da ke da rinjaye a Amurka, duk da cewa akwai sauran jam’iyyu a can.

"Muna so jam’iyyarmu ta zama wadda ke samun kaso 90 cikin 100 na ƙuri’un zaɓe. Sauran jam’iyyu za su iya samun kaso 10. Kowace jam’iyya na so ta bayar da gudunmawa ga al’umma, kuma ina ganin jam’iyyarmu na yin hakan."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya yi magana kan magajinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya taɓo batun wanda zai gaje shi idan ya kammala mulki a shekarar 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa kusan mutum 20 waɗanda suka nuna niyyar neman kujerarsa a zaɓen 2027 lokacin da wa'adinsa zai cika.

Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa Allah Madaukakin Sarki ne ke da ikon zaɓar wanda zai dare kujerar shi bayan ya sauka daga mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng