2023: Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APGA ya zaɓi mataimaki

2023: Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APGA ya zaɓi mataimaki

  • Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faɗi tashin neman mataimaki, Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA
  • Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023
  • A wata sanarwa da kungiyar yaƙin neman zaɓen Umeadi ta fitar, ta ce ta zaɓi Koli ne saboda kwarewarsa a ɓangaren walwalar mutane

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APGA a zaɓen 2023, Farfesa Peter Umeadi, ya zaɓi tsohon shugaban kwadugo, Kwamaret Abdullahi Muhammed Koli, a matsayin mataimaki.

Daily Trust ta rahoto cewa Wannan matakin ya biyo bayan wa'adin 17 ga watan Yuni wanda hukumar INEC ta bai wa jam'iyyun siyasa su miƙa mata sunayen yan takara da mataimakansu.

Umeadi, wanda ya kai matsayin Farfesa a ɓangaren shari'a a jami'ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) , ya rike muƙamin shugaban Alƙalai na jihar Anambra tsawon shekara Bakwai.

Kara karanta wannan

Kano: Gwanayen Alƙur'ani da dubbanin mutane sun gudanar da Addu'o'i ta musamman kan zaɓen 2023

Dan takarar APGA, Peter Umeadi.
2023: Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APGA ya zaɓi mataimaki Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Zaɓar Mista Koli a matsayin mataimaki na ƙunshe ne a wata sanarwa da ƙungiyar yaƙin neman zaben Umeadi ta fitar ranar Lahadi a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ɗan takarar ya zaɓi Muhammed Koli?

A cewar Sanarwan, ɗan takaran ya zaɓi Muhammed Koli ne saboda kwarewa, horo da sadaukarwan da ya ke da su kan jin daɗi da walwalar al'umma tsawon shekaru.

Wani ɓangaren sanarwan ya ce:

"Kwamaret Muhammed Koli na cikin waɗan da ke sahun gaba wajen fafutuka a ƙungiyar kwadugo kuma mutum me sadaukar da komai don walwalar al'umma."
"Ya jagoranci fafutuka da dama domin walwala da jin daɗin ma'aikata a matsayinsa na shugaban ƙungiyar kwadugo (NLC) reshen jihar Bauchi."

Har zuwa yau dai manyan jam'iyyun siyasar ƙasar nan na cigaba da faɗi tashin neman wanda zai zama mataimakin ɗan takarar su na shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa

A wani labarin na daban kuma Fasinjojin jirgin ƙasa Kaduna 11 da yan ta'ada suka sako sun dira Abuja

Mutane 11 daga cikin Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da aka sace, waɗan da yan ta'adda suka sako sun isa babban birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna cewa Fasinjoji 11 sun kubuta ne bayan tura wa yan ta'addan ƴaƴan su guda Takwas ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel