Kano: Jiga Jigai 4 Sun Rabu da Kwankwaso da NNPP, Kwankwasiyya Ta Yi Martani
Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun fara fice wa daga tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu daga cikin wadanda suka fice daga Kwankwasiyya sun dora alhakin hakan a kan rashin jituwa da rikicin cikin gida da ya ta’azzara a NNPP, musamman a Kano, yayin da wasu ke adawa da salon jagorancin Kwankwaso.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro wasu daga cikin jiga-jigan NNPP da suka bar tafiyar Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma martanin Kwankwasiyya kan illar hakan ga tafiyarsu.
Mafi akasarinsu, yan APC da suka sauya sheƙa zuwa tafiyar Kwankwasiyya a lokuta daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Alhassan Rurum ya bar Kwankwaso
Alhassan Rurum, shi ne dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa ya sanar da ficewarsa daga Kwankwasiyya a watan Nuwamba 2024, kuma ana zargin ya bar tafiyar ne saboda rushe masarautun Kano.
Rurum ya ce yana goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, amma yana marawa bangaren NNPP na Dr. Boniface Aniebonam a baya, yana zargin Kwankwaso da mallakar jam’iyyar don muradunsa na kashin kai.
2. Madakin Gini ya raba gari da Kwankwaso
Daily Trust ta wallafa cewa Aliyu Sani Madakin Gini, mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai da dan majalisar Dala, ya fice daga Kwankwasiyya a watan Nuwamba 2024.
A jawabin da ya yi wa magoya bayansa, ya caccaki salon shugabanci na Kwankwasiyya yana cewa an matsa ta fuskar jagoranci.
Ya kuma bukaci mabiyansa da su cire hular ja, yana mai cewa alamar nuna biyayya ce kawai, tare da shaida cewa yana shirye ya kara da duk wanda ya dauke shi a gaba.
3. Baffa Bichi ya rabu da Kwankwasiyya
Jam'iyya mai mulki ta NNPP ta dakatar da Dr. Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi ne sakataren gwamnatin jihar Kano a 2024.
The Guardian ta ruwaito cewa ko da yake jam’iyya ta ce an dakatar da shi ne saboda rashin biyayya, wasu rahotanni sun ce lamarin ba haka ya ke ba.
An yi zargin cewa Dr. Bichi yana daga cikin wadanda ke yunkurin kafa sabuwar tafiya a NNPP da ke kalubalantar rinjayar Kwankwaso a jam’iyyar.
A baya-bayan nan ne Baffa Bichi ya shiga tawagar su Kawu Sumaila wajen sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulki.
4. Kawu Sumaila ya sauya sheka daga Kwankwasiyya
Abdulrahman Kawu Sumaila, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisa, ya bar tafiyar Kwankwasiyya.
Sanata Kawu Sumaila, wanda a yanzu haka ya ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana cewa ya fi karfin NNPP ko Kwankwasiyya su yi masa gori.
Ya bayyana cewa ya bar NNPP zuwa APC ne saboda a nan ne zai fi samun damar samo wa mutanen da wakilta ayyukan ci gaba mai dorewa.
Yunusa Adamu Dangwani, tsohon kwamishinan ruwa a Kano ya sauya sheka zuwa APC mai rike da mulki a Najeriya.
Dr. Yunusa Adamu Dangwani wanda ya taba zama shugaban fadar Rabiu Kwankwaso ya bar tafiyar kafin 2023.
Bayan shekaru a jam'iyyar PDP da ya gaza samun tikitin takarar gwamna, ya dawo APC da nufin kara gwabzawa a zaben 2027.
'Ko a jikinmu,' Kwankwasiyya ta yi martani
A zantawarsa da Legit, Musa Gambo Danzaki, Shugaban Kwankwasiyya na jihar Kano ya ce fitar manyan yan siyasa daga cikin Kwankwasiyya ba zai yi wa tafiyar Rabi'u Musa Kwankwaso illa ba.

Asali: Facebook
Ya kara da cewa:
"Fitar wasu 'yan majalisu ko Sanata daga cikin Kwankwasiyya ba zai kawo nakasu ko tasgaro ko rauni a fadin jihar Kano ba."
"Hasali ma dama wadannan mutanen ba 'yan Kwankwasiyya ba ne, wasu mutane ne ne suka shigo Kwankwasiyya, don sun tabbatar da cewa bukatarsu ba za ta taba biya ba sai sun shiga Kwankwasiyya.
"Suka shigo Kwankwasiyya, bukatarsu ta biya, suka fita. Kuma a Kwankwasiyance ba su fita da kowane mutum daya dan Kwankwasiyya ba."
Ya kara da cewa ko a lokacin da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tarkata dukkanin mukarrabansa a Kano suka bar Kwankwasiyya, sai da NNPP ta kayar da gwamnati a zaben da ya zagayo.
NNPP ta yi magana kan korar Kwankwasiyya
A wani labarin, mun wallafa cewa jam'iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Ajuji Ahmed, ta musanta ikirarin cewa kotu ta dawo da tsagin Agbo Major a matsayin shugaba.
Tsagin Ajuji, wanda ke da alaka da Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, ya bayyana cewa har yanzu, su ne ke da shugabancin NNPP idan aka bi hukuncin.
A cewar Sakataren yada labaran jam'iyyar, Ladipo Johnson, NNPP ta ce tsagin Agbo Major yana ƙirƙirar ƙarya game da hukuncin kotu, domin cewa ta yi ba ta da hurumi a kan shugabanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng