"Mun Zama Jihohi 3," Gwamna Otu Ya Hango Abubuwan da ke Janye Gwamnoni zuwa APC
- Gwamna Bassey Otu ya ce kyakkyawan shugabancin Bola Ahmed Tinubu ne ya fara jawo hankalin gwamnoni da manyan ƴan siyasa zuwa APC
- Wannan kalamai na gwamnan Kuros Riba na zuwa ne bayan Gwamnan Delta da manyan jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a makon jiya
- Gwamna Otu ya ce a baya Kuros Riba ce kaɗai jihar da APC ke mulki a Kudu maso Kudu amma yanzu Edo da Delta sun haɗe da ita don kawo ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Bassey Otu, ya ce tururuwar da manyan ƴan siyasa ke yi zuwa APC na da nasaba da ayyukan alherin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi.
Gwamna Otu ya bayyana cewa ko kaɗan yawan shiga jam'iyyar APC da ake yi ba shi da nasaba da lissafin siyasa, illa kawai mutane sun gamsu da nasarorin Shugaba Tinubu.

Asali: Facebook
Otu ya fadi haka ne yayin taron karbar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma APC a hukumance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje; da gwamnonin APC daga jihohi daban-daban.
Meyasa gwamnoni da ƴan siyasa ke shiga APC?
Gwamna Otu ya bayyana shiga APC da Gwamna Oborevwori ya yi a matsayin matakin da ya dace, wanda ke nuna burin al’ummar jihar Delta, ci gaban yankin Neja Delta da karfafa Najeriya gaba daya.
Ya ce Kuros Riba, wadda ke zaman kadaici a matsayin jihar da APC ke mulki a yankin Kudu maso Kudu tsawon lokaci, yanzu tana alfahari da hada tutar ci gaba da jihohin Delta da Edo a inuwa ɗaya.
A ruwayar Vanguard, Gwamna Bassey Otu ya ce:
“Karuwar yawan jihohin Kudu maso Kudu da APC ke mulki wani buri ne muke da shi tun a baya wanda a yanzu ya fara zama gaskiya.”
Gwamna Otu ya yabawa salon mulkin Tinubu
Gwamna Otu ya bayyana salon shugabancin Bola Tinubu a matsayin mai nagarta wanda ke kawo sauyi a rayuwar ƴan ƙasa.
A cewarsa, mulkin Tinubu ya kawo sauyi daban-daban wanda suka haɗa da farfaɗo da ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da sauransu.

Asali: Twitter
Da yake tsokaci kan sauya shekar Oborevwori tare da magabacinsa, Ifeanyi Okowa, da manyan ’yan PDP a Delta, Otu ya ce sun kafa tarihi a yankin Neja Delta.
Ya ce wannan sauya sheƙa da suka yi a lokaci guda ta shiga tarihi kuma za ta taimaka wajen inganta haɗin gwiwa a yankin, bunƙasa tattalin arziƙi da daidaiton siyasa.
Okowa ya yi nadamar takara tare da Atiku
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa ya yi nadamar takarar mataimakin shugaban ƙasar da ya yi a 2023.
Okowa ya ce mutanensa ba su yarda da amincewar da ya yi na zama abokin takarar Atiku Abubakar ba a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.
Ganin Arewa ke mulki tun 2015, tsohon gwamnan ya ƙara da cewa takarar da ya yi da Atiku ya jawo masa baƙin jini da illa a siyasa ƙafin ya ankara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng