2027: Tinubu Ya Kara Karfi a Arewa, Magoya bayan Atiku, Kwankwaso Sun Koma APC
- Wasu magoya bayan PDP da NNPP sun sauya sheƙa zuwa APC a Jigawa, inda Gwamna Umar Namadi ya tarbe cikin farin ciki
- Gwamna Namadi ya tabbatar wa sababbin mambobin adalci da damar bada gudummawa, yana mai ƙarfafa su su yada manufofin APC
- Jagoran masu sauya sheƙar, Idris Maikura, ya ce sun ga ayyukan Namadi kuma sun yarda APC ce mafita ta ci gaban jihar Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Wasu magoya bayan jam’iyyun adawa na PDP da NNPP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa.
Gwamna Umar Namadi ne ya tarbi masu sauya shekar zuwa APC, yana mai nuna farin cikinsa da ƙarin goyon baya da jam'iyyar ke samu a jihar.

Asali: Twitter
Jigawa: Magoya bayan PDP, NNPP sun koma APC
Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan PDP da NNPP sun sanar da sauya shekarsu ne a taron gwamnati da mutanen gari karo na shida da aka gudanar a Buji, a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa ana gudanar da taron "gwamnati da mutanen gari" domin bai wa jama'a damar tattaunawa da gwamnati, su fada mata damuwarsu, da kuma ba gwamnatin damar fadin nasarori da shirye-shiryen da take da su.
A yayin taron, Gwamna Namadi ya shaida wa wadanda suka sauya cewa APC na maraba da su zuwa jam'iyyar, kuma daga yanzu sun zama "yan gida."
A cewar gwamnan:
“Wannan sauya sheƙar shaida ce ga kyakkyawan aikin da muke yi a Jigawa. Za mu ci gaba da inganta jihar kamar yadda muka yi alkawari."
Sakon gwamnan Jigawa ga sababbin 'yan APC
Gwamnan ya tabbatar wa da masu sauya sheƙar cewa za a yi musu adalci, daidaito, da kuma bai wa kowa dama cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa:
“Za mu tabbatar da cewa an bai wa kowa dama daidai wa daida, kuma kofa a bude take ga kowa don ba da gudummawa wajen bunƙasa jam’iyyar.".
Hakazalika, Gwamna Namadi ya bukaci sababbin mambobin da su ci gaba da ba da shawara masu amfani, tare da yada manufofi da kudurin jam'iyyar APC a cikin al'ummominsu.
Gwamnan na Jigawa ya ce:
“Zuwan ku zai taimaka wajen gina jam’iyya mafi ƙarfi da haɗin kai domin cika alkawuran da muka dauka ga mutanen Jigawa.
“Muna buƙatar goyon bayanku da shawarwarinku domin ɗora Jihar Jigawa a sabuwar turba ta ci gaba kamar yadda muka dora tubalin hakan."

Asali: Twitter
Dalilin 'yan NNPP, PDP na komawa APC a Jigawa
Tun da fari, jagoran waɗanda suka sauya sheƙar, Idris Maikura daga Unguwar Maina, gundumar Chirbun, ya bayyana dalilansu na komawa APC.
Maikura ya ce:
“Mun ga kyakkyawan aikin da Gwamna Umar Namadi ke yi, kuma mun gaskata cewa APC ce mafi dacewa da burinmu na ci gaban al'umma.
“Muna da yakinin cewa APC za ta ɗora Jigawa kan sabon matakin ci gaba, kuma muna farin cikin kasancewa cikin wannan jam'iyya."
Wannan sauya sheƙar ya jawo martani daga sassa daban-daban, inda shugaban PDP na jihar, Ali Diginsa, ya bayyana rashin jin daɗinsa yayin wata tattaunawa ta waya manema labarai.
Tasirin Atku a siyasar Najeriya
Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban kasa sau da dama, kuma duk babu wanda ya yi nasara a tarihin siyasarsa, lamarin da ke kara daukar hankalin al'umma.
A zaben da ya gabata na 2023, Atiku ya fito na uku, inda ya zo kusa da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a zaben mai tarihi.
A matsayinsa na gaba-gaba a jam'iyyar adawa, yanzu haka jam'iyyar ta PDP na ci gaba da samun rashin karbuwa a yankuna daban-daban na kasar nan.
Gwamnan Kebbi ya karyata shirin barin APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya musanta jita-jitar cewa shi da wasu gwamnoni hudu suna shirin barin PDP zuwa APC.
Yayin da yake kiran wannan jita-jitar da "tatsuniyar baragurbin 'yan siyasa", Gwamna Idris ya bayyana cewa zai kasance a cikin APC har sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.
Duk da cewa APC ce mai mulki a Kebbi, amma rahoto ya nuna cewa PDP na da tasiri sosai a jihar, kasancewar dukkanin sanatocin jihar na karkashin jam’iyyar adawar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng