Hakeem Baba Ahmed: Tsohon Hadimin Kashim Ya Fadi Matsayar Arewa kan 2027

Hakeem Baba Ahmed: Tsohon Hadimin Kashim Ya Fadi Matsayar Arewa kan 2027

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmed ya ce Arewa za ta yanke shawara kan zaben 2027 a cikin watanni shida
  • Dr. Hakeem Baba Ahmed ya kuma yi tinƙaho da cewa babu wanda zai yi nasara a zaben shugaban ƙasa ba tare da Arewa ba
  • Ya ce Arewa ta tsinci kanta a cikin tsaka mai wuya, saboda haka ba za a lamunci siyasar addini da kabilanci a zaben gaba ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Tsohon mai bai wa Kashim Shettima shawara na musamman kan harkokin siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana a kan shirin zaben shugaban kasa

Ya bayyana cewa shiyyar Arewa za ta bayyana matsayarta wajen zaben shugaban kasa na 2027 a cikin watanni shida masu zuwa.

Tinubu
Tsohon hadimin Tinubu ya ce Arewa za ta fitar da dan takara Hoto: @baba_hakeem/Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a wani taro da aka shirya tare da tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Arewa ta gaji da siyasar nuna bambanci na kabilanci da addini, kuma lokaci ya yi da za ta zabi shugabanci bisa cancanta da nagarta.

"Arewa za ta tsaya da kafarta" Tsohon hadimin Kashim

Channels Tv ta ruwaito Baba-Ahmed, wanda ya taba zama shugaban ma’aikatan tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokaci ya yi da Arewacin Najeriya za ta tsaya da kafarta.

Ya ce:

“A cikin watanni shida, Arewa za ta yanke shawarar inda za ta tsaya – ko da akwai goyon baya daga sauran sassan ƙasar, ko babu.
Idan sauran yankuna za su haɗu da mu, to madalla. Idan ba haka ba, za mu ci gaba da tafiyarmu. Abu daya ya tabbata: Ba wanda zai zama shugaban ƙasa ba tare da goyon bayan Arewa ba.”

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya nuna damuwarsa kan halin da ƙasar ke ciki, ya shawarci ’yan Arewa su guji siyasar ruɗu, musamman yayin da ake shirin shiga babban zaɓe.

Hakeem Baba Ahmed: “Arewa ta sha wahala"

Da yake tunawa da abubuwan da suka faru a baya, Baba-Ahmed ya ce Arewa ta sha wahala sosai a lokacin ta’addancin Boko Haram wanda ya shafi Musulmai da Kiristoci da Fulani da Baju da sauran ƙabilu.

Ya ce:

“Kafin Buhari ya zama shugaban ƙasa, Boko Haram na fashe masallatai da coci-coci da wurare a Abuja da Legas. Wannan ne lokacin da ’yan Arewa suka fahimci bukatar hadin kai. Yanzu, babu wani ɗan siyasa da zai bayyana kawai kuma ya ɗauka cewa za a bi shi. Waye kai?”

“Ana tauye Arewa” – Hakeem Baba-Ahmed

Baba-Ahmed ya gargadi gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da kada su ci gaba da wulakanta Arewa, yana mai cewa hakan na iya jawo mata matsala.

Ya ce:

“Idan suna shirin yin maguɗi a zabe, su yi hattara. Ba zai yi wa Najeriya daidai ba. Arewa na kallo. Dattawa, talakawa da kungiyoyi za su ce 'ya isa'. Wannan zalunci da watsi da yankin Arewa sai an daina.”

Ya kuma bukaci al’ummar Arewa da su fita daga siyasar addini da ƙabila, su duba cancanta da gaskiya wajen zaɓar shugabanni.

Hakeem Baba-Ahmed ya ce ’yan Arewa sun koyi darasi daga zabukan da suka gabata, kuma za su shiga zaben 2027 da sabon tunani da hangen nesa.

Hadimin Tinubu ya soki El-Rufa'i

A baya, kun ji cewa Daniel Bwala, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya sake sukar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Bwala ya dage a kan cewa tsohon gwamnan Kaduna da ya bar APC ba shi da ƙarfi ko yawan magoya baya da tasirin da zai iya kawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga kan mulki.

Wannan ya biyo bayan yawan sukar da El-Rufai ke yiwa daga cikin mukarraban gwamnatin Tinubu da yanayin mulkinta, lamarin da ya jawo cece-kuce a fagen siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.