'Yan Bindiga Sun Bakunci Lahira, Sojoji Sun Kwato Kayan da Suke Yaudarar Jama'a da Su
- Dakarun Operation Fansan Yamma sun ƙwato kayan sojoji 106 da ake zargin an tanadar wa ’yan ta’adda a jihar Zamfara
- An kashe wasu mutane biyu da ake zargi ’yan ta’adda ne yayin samamen da aka gudanar a ƙaramar hukumar Tsafe
- A wani samame daban a Kaduna, dakarun sun ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi tare da ƙwato kayan ayyukan ’yan ta’adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yammaq1 sun ƙwato kayan sojoji guda 106 da ake zargin an tanadar wa ’yan ta’adda a jihar Zamfara.
Haka kuma, dakarun sun kashe wasu mutane biyu da ake zargi ’yan ta’adda ne yayin samamen.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa mukaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, Kyaftin Tamuno Sinivie, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Gusau.
Sojoji sun kashe yan bindiga 2
Sinivie ya ce dakarun sashe na biyu sun gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan yadda ’yan ta’adda ke safarar kayan sojoji.
Ya ce dakarun sun gudanar da samamen ne ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, 2026, a garin Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
A yayin aikin, dakarun sun kashe mutane biyu da ake zargi ’yan ta’adda ne tare da ƙwato kayan da ake safarara zuwa yan bindiga.
Kayan sojojin da aka ƙwato
Sinivie ya ce kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da, kayan sojoji masu kama da na rundunar soja guda 26, rigunan sojoji 26 da hulunan yaki masu kama da na sojoji guda 54
Ya ce samamen na daga cikin ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na tarwatsa hanyoyin samar da kayayyaki da kayan aiki ga ’yan ta’adda.
A cewarsa, ’yan ta’adda na amfani da kayan sojoji wajen yin kama da jami’an tsaro, yaudarar mutane a shingayen bincike da kuma samun damar zirga-zirga cikin sauƙi yayin kai hare-hare.
An ceto mutum a Kaduna
A wani samame na daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun sashe na farko sun mayar da martani kan kiran neman agaji daga al’ummar Kutura da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Dakarun sun bi sawun ’yan ta’addan tare da fafatawa da su, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Sinivie ya ce:
“Bayan wani bincike da aka gudanar a yankin, an samu nasarar ceto ɗaya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato wasu kayan ayyukan ’yan ta’adda daga maboyarsu.”

Source: Facebook
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Sinivie ya buƙaci jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu da suka gani na shakku a yankunansu cikin gaggawa.
Yan bindiga sun kashe malamai a Zamfara
Kun ji cewa ’yan bindiga sun kashe malamai biyu a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara , yayin da suka yi garkuwa da wasu mazauna yankin 13.
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da hare-haren biyu a cikin bayanan ayyukan tsaro da ta fitar a faɗin ƙasar ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026.
Asali: Legit.ng

