An Umarci Korar Fulani daga Jihar Kebbi? Mun Samu Cikakken Bayani

An Umarci Korar Fulani daga Jihar Kebbi? Mun Samu Cikakken Bayani

  • Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi ya ce babu wani umarni da aka bayar na korar Fulani daga karamar hukumar Sakaba
  • Ya bayyana cewa an yi kuskuren fassara kalaman shugaban karamar hukumar Sakaba, inda aka bukaci miyagun mutane su bar yankin ba tare da la’akari da kabilarsu ba
  • Salihu Maikasuwa Dangoje ya bukaci al’umma su kwantar da hankulansu, yana mai cewa an samu zaman lafiya bayan barin wasu miyagun mutane yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Kebbi - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Salihu Maikasuwa Dangoje ya yi magana kan rahoton korar Fulani a Kebbi.

Dangote ya bayyana cewa babu wani umarni ko umarnin hukuma da aka bayar na tilasta wa Fulani barin karamar hukumar Sakaba.

An musanta rahoton korar Fulani a Kebbi
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi. Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
Source: Facebook

Dangoje, wanda dan asalin karamar hukumar Sakaba ne kuma yake wakiltarta a majalisar dokokin jihar, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Bayan tara malamai 2000, Barau Jibrin ya haɗa kan sarakuna 3000 saboda Tinubu da Abba

Korar Fulani: Kakakin Majalisa ya yi martani

Kakakin majalisar ya yi wannan karin haske ne bayan wani labari da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka yi zargin cewa shugaban karamar hukumar Sakaba, Dauda Sakaba, ya bayar da umarnin korar Fulani mazauna yankin.

Ya ce abin da ya faru kuskure ne wajen fahimtar kalaman shugaban karamar hukumar, yana mai jaddada cewa Arewacin Najeriya gida ne ga al'ummar Fulani, don haka ba daidai ba ne a ayyana su a matsayin mutanen da ba a bukata.

Dangoje ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga hare-hare da sace-sacen mutane da ake yi a Sakaba, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankunan da abin ya shafa yin kaura zuwa Dirindaji, hedikwatar karamar hukumar, domin neman mafaka.

Ya ce an kira taron masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalar tsaro, inda aka cimma matsayar cewa dukkan miyagun mutane da ke zaune a Dirindaji su bar garin kafin daukar wani mataki mai tsauri.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya goyi baya na kare kasar Yarabawa daga 'yan ta'adda,' Sunday Igboho

An ƙaryata musanta korar Fulani a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Asalin manufar sanarwar da ake yadawa

A cewarsa, sanarwar ba ta shafi Fulani kadai ba, domin ta hada da dukkan kabilun da ke yankin, ciki har da Hausawa, Dakarkari, Fulani, Kambari da Dukkawa.

Ya ce bayan sanarwar, wasu mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka daga cikin wadannan kabilu sun fice daga garin, wanda hakan ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kuma kawo karshen hare-haren 'yan bindiga da kungiyoyin ta'addanci.

Kakakin majalisar ya kuma nemi afuwa kan kalaman da aka danganta ga shugaban karamar hukumar Sakaba, Dauda Sakaba, tare da kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu.

Dangoje ya bukaci al'umma su mayar da hankali kan shirye-shiryen babban zaben da ake sa ran gudanarwa a watan Janairun 2027, cewar Vanguard.

Gwamna ya yi wa Tinubu alkawari a 2027

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Nasir Idris ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa jihar Kebbi za ta ci gaba da kasancewa tare da APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ciyaman ya yi martani ga Amnesty game da kalaman barazana da ya yi kan zaɓen APC

Dr. Nasir Idris ya ce jihar ba ta taɓa ba Tinubu kunya ba, kuma za ta ƙara masa ƙuri’u fiye da waɗanda ta ba shi a zaɓen 2023.

Gwamnan ya roƙi Tinubu ya taimaka wajen fara gudanar da ayyukan tashar jigilar kaya ta cikin ƙasa ta Samia da ke Bagoro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.