Jerin Manyan 'Yan Siyasar da Sauya Sheka zuwa APC Ya Kare su Daga Binciken EFCC
Sauyin sheka da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da daukacin jiga-jigan PDP suka yi zuwa APC ya girgiza harkokin siyasar Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da hukumar EFCC ke bincikensa bisa zargin karkatar da makudan kudade.
Wannan al’amari ya tunatar da irin yadda wasu fitattun 'yan siyasa suka canza sheka zuwa jam'iyyar APC bayan sun shiga matsala da EFCC.
A lokuta da dama, wannan sauya sheka ka iya zamewa ‘yan siyasa mafakar kaucewa tuhuma da bincike mai zurfi na hukumar ta EFCC.

Asali: Twitter
Ga cikakken bayani kan wadannan ‘yan siyasa kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Godswill Akpabio
A shekarar 2015 ne hukumar EFCC ta fara binciken Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, bisa zargin wawure Naira biliyan 108.1 lokacin da yake kan mulki tsakanin 2007 zuwa 2015.
Binciken ya samo asali ne daga korafin wani lauya, Leo Ekpenyong, wanda ya ce Akpabio tare da wasu jami’an gwamnati sun karkatar da kudaden jihar.
Duk da yake ya zama sanata kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai a lokacin, hakan bai hana EFCC ci gaba da bincikensa ba.
A shekarar 2018, Akpabio ya sauya sheka zuwa APC a hukumance. Bayan sauyin shekarsa, kodayake EFCC ta ce bincike yana nan, maganar ta lafa.
Daga bisani, Akpabio ya zama minista sannan a 2023 aka zabe shi Shugaban Majalisar Dattijai.
2. Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia, ya fara fuskantar tuhumar EFCC tun shekarar 2007 bayan yagewar rigar kariyarsa ta mulki.
Hukumar ta tuhume shi da karkatar da makudan kudade ta hannun kamfaninsa, Slok Nigeria Ltd., da kuma Udeh Udeogu, tsohon daraktan kudi na gidan gwamnati.
A yayin da shari’arsa ke gudana, Kalu ya sauya sheka daga jam’iyyar PPA zuwa APC. Duk da ya fuskanci zarge-zarge 34 na almundahana, ya ci gaba da rike mukami.
A shekarar 2019, wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari. Sai dai, a 2020, Kotun Koli ta soke hukuncin saboda dalilai na fasaha, ba wai saboda an wanke shi ba.
3. Stella Oduah
Stella Oduah, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, ta gamu da shari’a bayan EFCC ta zarge ta da sace kudi har Naira biliyan 5 a 2020.
Bayan da aka fara shirin cafke ta a kotu a 2021, Oduah ta koma jam’iyyar APC. Sai dai kasancewarta a APC bai dade ba, domin ta dawo PDP a zaben 2023.
A yanzu haka, shari'arta na ci gaba a kotu inda take fuskantar tuhume-tuhume masu nauyi kan harkokin kudade lokacin da take minista.
4. Musiliu Obanikoro
Musiliu Obanikoro, tsohon ministan tsaron cikin gida, ya gamu da matsala bayan EFCC ta tuhume shi da karbar Naira biliyan 4.7 daga ofishin tsohon NSA a 2014 domin gudanar da zabuka a jihohin Ekiti da Osun.
Bayan an kama shi a 2016, an bayar da belinsa, daga bisani ya sauya sheka zuwa APC a 2017.
Tun bayan sauyin shekar, Obanikoro ya kasance shaida a shari’un da suka shafi badakalar kudade, musamman a shari'ar da ake yi wa Sambo Dasuki da Ayodele Fayose.
5. Peter Nwaoboshi
A shekarar 2021 ne EFCC ta fara tuhumar sanata Peter Nwaoboshi da laifin sace makudan kudaden kasa.
Kotun farko ta wanke shi, kuma mako guda bayan haka ya sauya sheka zuwa APC. Duk da cewa daga bisani kotun daukaka kara ta sami Nwaoboshi da laifi, ya arce ya guje wa kamun hukuma.
Bayan jinkiri da rikice-rikicen shari’a, Kotun Koli ta sake wanke shi daga zarge-zargen da ake masa.
6. Emmanuel Bwacha
Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai daga Taraba ta Kudu, Emmanuel Bwacha, shima ya fuskanci zarge-zarge daga EFCC kan yadda aka kashe kudaden ayyukan mazabarsa.
A shekarar 2021, wasu daga cikin mazabarsa suka bukaci EFCC ta bincike shi kan yadda aka kashe kudade tsakanin 2017 zuwa 2020.
A 2022, Bwacha ya sauya sheka zuwa APC. Sai dai sauyin shekar ya janyo masa matsala domin wata kotu ta soke kujerarsa a majalisar dattijai.
Duk da haka, ya nemi tsayawa takarar gwamnan Taraba, amma rikicin cikin gida ya hana shi samun tikitin jam’iyyar.
EFCC ta ki bayar da cikakken bayani
Kokarin jin ta bakin hukumar EFCC kan ci gaba da binciken Okowa da sauran 'yan siyasa da suka koma APC bai samu nasara ba, kamar yadda FIJ ta bayyana a rahotonta.
Duk da kokarin da aka yi na tuntubar kakakin hukumar, Dele Oyewale, bai bayar da amsa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Sai dai, ba sabon abu bane samun wadatattun bayanai daga hukumomin gwamnati, lamarin da ke nuna Rashin maida hankali ga aikin da aka dauke su.
Asali: Legit.ng