Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

  • Jam'iyyar APC ta samu sabon Sanata daya daga jihar Anambara
  • Gwamnonin APC 3 da mataimakin shugaban majalisa suka tarbeta
  • Wannan na faruwa ana saura yan makonni zaben gwamnan jihar Anambra

Abuja - Tsohuwar Ministar sufurin jirgin sama, kuma Sanata mai wakiltar Anambra a majalisar dattawa, Stellah Oduah, ta fita daga jam'iyyar People Democratic Party (PDP).

Bayan fitar ta, Stella Oduah ta sanar da manema labarai komawarta jam’iyyar APC

Oduah tayi wannan sanarwa ne a zaman da tayi da shugaban kwamitin rikon kwaryan APC kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

Daga cikin wadanda ke zaman akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege; gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma; da Sanata Andy Uba.

Kalli hotunan:

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Rikicin Shugabancin PDP Ya Ƙare, an Nada Sabon Shugaba Na Kasa

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC
Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: AIT Onine
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC
Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: AIT Online
Asali: Facebook

INEC Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta canza sunan Michael Umeoji, zuwa Chukwuma Soludo, a matsayin ɗan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar APGA.

Hakazalika, INEC ba ta sanya jam'iyyar PDP ba a jerin waɗanda ta tantance zasu fafata a zaɓen gwamnan dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba 2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, Festus Okoye, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng