Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari

Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta sake karfi yayin da ta tarbi sabon mamba, Sanata Peter Nwaoboshi, daga jam’iyyar adawa ta PDP
  • Nwaoboshi, sanatan da ke wakiltar yankin Delta ta Arewa, ya gana da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa a ranar Juma'a, 25 ga Yuni
  • Sauya shekar Sanatan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan PDP ta sanar da cewa ta dakatar da shi bisa zarginsa da ayyukan adawa da jam’iyyar

Sanata Peter Nwaoboshi ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives (APC) mai mulki.

An bayyana sauya shekar sanatan wanda ke wakiltar yankin Delta ta Arewa a Majalisar Tarayya a lokacin da ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni. Ya hadu da Shugaba Buhari a ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai

Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari
Sanata Peter Nwaoboshi ya gana da Shugaba Buhari Hoto: Tolani Alli
Asali: UGC

Tolani Alli, mai daukar hoton fadar shugaban kasa da ke aiki a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya yada hotunan sanatan yayin da ya gana da Shugaba Buhari tare da shugaban riko na kasa na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai kuma dan majalisa mai wakiltar Delta ta Tsakiya, Ovie Omo-Agege shima ya kasance a wajen yayin da Sanata Nwaoboshi ya gana da shugaban kasar.

PDP ta dakatar da Sanata Nwaoboshi

Kafin sauya shekarsa, Legit.ng ta rahoto cewa biyo bayan zarge-zargen da ake yi masa na ayyukan da suka saba jam’iyya, reshen jihar Delta na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta dakatar da Sanata Peter Nwaoboshi.

An dakatar da dan majalisar mai wakiltar Delta ta Arewa na tsawon wata daya a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar, Dr. Ifeanyi M. Osuoza wanda ya sanar da dakatarwar ya ce an yanke hukuncin ne a taron gaggawa na Kwamitin Aiki na jam’iyyar a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel