"Gwamnatin Tinubu Ce Mafi Muni a Tarihi," El Rufai Ya Tabo Batun Tsaro a Najeriya
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da zama mafi muni a cin hanci da nuna kabilanci a tarihin kasar
- El-Rufai ya ce gwamnati na amfani da ƙarya da farfaganda wajen yaudarar mutane, inda ake ɓoye gaskiya kan matsalolin tsaro da tattali
- Tsohon gwamnan na Kaduna ya jaddada cewa SDP za ta karɓi mulki a 2027, yana mai cewa yanzu ita ce jam’iyyar da ake maraba da ita a ko ina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da zama mafi muni a cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a daren Litinin a Katsina, inda ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu da 'nuna kabilanci' a rabon mukamai.

Asali: Facebook
El-Rufai ya caccaki Tinubu kan 'kabilanci'
A wani bidiyo da DW Hausa ta wallafa, wanda Legit Hausa ta gani, an ji El-Rufai na cewa gwamnatin Bola Tinubu ce mafi kwarewa a iya farfaganda da yada karya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar tsohon gwamnan na Kaduna, gwamnatin tarayya karkashin Tinubu na amfani da karya, farfaganda wajen yaudarar mutane kan cewa an samu nasara kan tsaro.
"Tun da Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya, Najeriya ta fara komawa baya. Rashin tsaro ya karu, tattalin arziki ya mutu, mutane attajirai sun tsiyace.
"Sannan ga kabilanci wurjanjan. Mutum ya tashi, ba wanda zai ba babban mukami a gwamnati sai wanda ya sani ko dan kabilarsa.
"Wannan irin zalunci da kabilanci da sata da muka ga ana yi ba abin da jam'iyyar APC aka yi ta a haka ba."
- A cewar El-Rufai.
El-Rufai ya soki Tinubu kan tsaro
Tsohon gwamnan na Kaduna, wanda ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa, ya musanta ikirarin gwamnatin arayya na cewa tsaro ya inganta a kasar.
El-Rufai ya bayyana cewa rashin tsaro da ake fama da shi a yanzu ya samo asali ne daga gazawar gwamnatin tarayya wajen fuskantar matsalar tsaron tun daga tushe.
Ya ce har yanzu akwai kananan hukumomi da dama a jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto da ke karkashin ikon ‘yan bindiga, kuma fitattun 'yan bindiga kamar Dogo Gide, Mallam Abba da Bello Turji suna na a raye.
A cewarsa:
“Na taba fada a baya cewa wannan gwamnatin Tarayya ce mafi muni a tarihin Najeriya, kuma dukkan alamomi sun tabbatar da hakan. An fi samun cin hanci da rashawa a gwamnatin nan.
“Suna cewa tsaro ya inganta a Najeriya, suna fadin sunayen ‘yan bindigar da suka kashe, sai dai manyan shugabanni irin su Dogo Gide, Mallam Abba da Bello Turji na nan da ransu.”
E-Rufai ya magantu kan tasirin SDP

Asali: Twitter
Mallam Nasiru El-Rufai ya kara da cewa:
“A Kaduna, Dogo Gide yana nan, Mallam Abba na Boko Haram yana raye, Bello Turji ma yana nan. Amma kullum sai ka ji an kashe shugabannin ‘yan bindiga, kuma ana cewa tsaro ya inganta."
Ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu kananan hukumomi a Katsina, Zamfara da Sokoto, yana mai cewa tsaro bai inganta ba, inji rahoton ThisDay.
El-Rufai ya kuma jaddada cewa jam’iyyarsa ta SDP, za ta kafa gwamnati a matakin tarayya da jihohi a zaben 2027 kuma ita ce yanzu jam'iyyar siyasa mafi karbuwa a Najeriya.
Kalli wani bangare na hirar El-Rufai a nan kasa:
El-Rufai ya zargi Ganduje da rashin girmama Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce sauyawar akidar APC ne ya sa ya fice daga jam'iyyar domin kare muradun talakawa.
El-Rufa’i ya kuma zargi shugabannin jam’iyyar APC da watsi da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tun bayan saukarsa daga mulki.
Ya ce shugaban jam’iyyar APC na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, bai girmama Buhari ba, har ma yana fadin maganganu masu zagi a kansa.
Asali: Legit.ng