Sufeto-Janar na 'yan sanda Adamu: Zan iya zama daram a ofis har zuwa 2023 ko 2024
- Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya ya kalubalanci karar da ake a kansa na karin wa'adin aiki
- Sufeton ya bayyana cewa, yana da damar zama a ofis har zuwa 2023 ko 2024 kamar yadda doka ta tanada
- Hakazalika ya bayyana dalilansa na fadin haka da cewa, an bashi matsayin ne a shekarar 2019
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya fada wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa doka ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a ofis har zuwa 2023 ko 2024.
Ya fadi haka ne a cikin takardun kotu da ya gabatar don kalubalantar karar da ke kalubalantar karin wa'adin watanni uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi a watan Fabrairu.
Premium Times a ranar Litinin ta samu takardar kin amincewar ta farko tare da rakiyar takaddun da Sufeton ya gabatar ta hannun lauyan sa, Alex Izinyon, wani Babban Lauyan Najeriya.
Mista Adamu ya cika shekaru 35 a kan aiki a ranar 1 ga Fabrairu, amma ya samu karin wa'adin watanni uku daga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 3 ga Fabrairu.
KU KARANTA: Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya
An ruwaito cewa wani lauya mazaunin Abuja, Maxwell Opara, ya shigar da kara a ranar 3 ga Fabrairu don kalubalantar tsawaita wa’adin.
Mista Opara ya yi jayayya a karar sa cewa ta hanyar sashi na 215 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma sashi na 7 na Dokar 'Yan Sandan Najeriya, 2020, Mista Adamu ba zai iya ci gaba da aikinsa ba kasancewar ya kamata ya yi ritaya a watan.
Amma Mista Adamu ya musanta hakan ta bakin lauyansa, cewa lokacin nasa bai kare ba a ranar 1 ga Fabrairu.
Sufeton ya yi jayayya cewa sabon dokar 'yan sandan Najeriya ta ba shi wa'adin shekaru hudu wanda ba zai kare ba har 2023 ko 2024.
A cewarsa, wa'adinsa zai kare a 2023 idan aka kirga shi daga 2019 lokacin da aka nada shi a matsayin Sufeto-Janar na 'yan sanda, ko 2024, idan aka kidaya daga 2020 lokacin da sabuwar dokar 'yan sandan Najeriya ta fara aiki.
KU KARANTA: Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta
A wani labarin, Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci jami’an rundunar‘ yan sanda ta Najeriya da su jajirce tare da nuna rashin tausayi akan “masu aikata laifuka”, Daily Trust ta ruwaito.
Adamu ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar, da ke Abuja, yayin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro, wanda aka sanya wa suna “Operation Puff Adder II”, don karfafa yakin da ake yi da ‘yan fashi, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kasar.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng