Hadakar Atiku Ta Gano 'Aikin' da Gwamnonin PDP ke Yiwa Shugaba Tinubu
- Hadakar da Atiku Abubakar ke jagoranta ta ce gwamnonin PDP na gurgunta adawa, kuma suna taimakon APC ta ci gaba da mulkin Najeriya
- Mai magana da yawun hadakar, Salihu Moh. Lukman, ya ce gwamnonin sun zama ’yan amshin shatar APC, kuma za su kawo nakasu ga yunkurinsu
- Ya ƙara da cewa, matuƙar ana son a kifar da gwamnatin Bola Tinubu a 2027, dole ne a haɗa kai wuri guda domin samar da adawa mai ƙarfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hadakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ke jagoranta ta caccaki gwamnonin jam’iyyar PDP.
Hadakar ta zargi gwamnonin da karɓar ikon wasu sassa na jam’iyyar PDP tare da kashe ƙoƙarin adawa a ƙasar tare da yiwa Tinubu aiki gabain 2027.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard, ta ruwaito cewa wannan na kunshe a cikin sanarwar da hadakar ta fitar a ranar Laraba ta mayar da martani ne ga matsayar da gwamnonin PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A taron da gwamnonin suka yi a ranar Litinin, 14 ga watan Afrilu, 2025, gwamnonin sun barranta kansu da kawancen jam'iyyu domin fitar da Tinubu daga ofis.
'Hadakar Atiku ce mafita,' Salihu Lukman
Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun hadakar, Salihu Moh. Lukman, yana cewa hadakar na da cikakkiyar damar doke APC da Tinubu, tare da ceton dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ya ce:
“Fiye da shekara 10 da PDP ta bar daga mulki, ’yan Najeriya na jiran jam’iyyar ta farfaɗo domin ta zama adawa mai ƙarfi. Sai dai abin da aka gani, jam’iyyar ta shiga wani yanayi."
“Gwamnonin PDP sun san cewa cutar da ke damun jam’iyyar ba ta da magani. Sun san cewa ’yan Najeriya ba za su karɓi PDP a matsayin madadin APC ba."

Kara karanta wannan
Kotu ta yi zama, za a yanke hukunci kan tuhumar Ganduje da karkatar da kuɗin Kano
Hadakar Atiku ta dura a kan Wike
Salihu ya ce Nyesom Wike, babban minista a gwamnatin Tinubu, ya samu karfi ne saboda rawar da ya taka wajen hana PDP gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.

Asali: Twitter
Lukman ya ce babban burin hadakar shi ne ceto dimokuraɗiyyar Najeriya, wanda ya haɗa da dawo da amincewa tsakanin ’yan ƙasa da shugabanni.
A cewarsa, hadakar ta zama wajibi idan ana so a dawo da mutuncin jam’iyyun siyasa da gina gasa ta siyasa a Najeriya.
Ya ce babu abin da ke nuna tabarbarewar dimokuraɗiyyar Najeriya fiye da halin da PDP ke ciki bayan ta mulki Najeriya a baya.
Atiku ya saba da gwamnonin PDP
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce kafa ƙawance ce kadai hanya mafi inganci da za ta iya tumbuke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Atiku ya yi wannan furuci ne ta bakin hadiminsa na musamman, Paul Ibe, inda ya ce matsayar gwamnonin PDP ta nuna bukatar ƙarin fahimta da tuntuba a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.
Kalamansa na zuwa ne bayan gwamnonin PDP ƙarƙashin jagorancin gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, sun bayyana cewa ba za su shiga kowace haɗaka ko ƙawance ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng