Ganduje Ya Yi Martani ga Buba Galadima da Ya Kira Shi 'Mara Amfani a Siyasa'
- Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya mayar da martani kan kalaman Buba Galadima na cewa ba shi da amfani a siyasa
- Cif Oliver Okpala, babban mai taimakawa Ganduje, ya bayyana cewa Buba Galadima mutum ne da ake yi wa kallon rashin daraja a siyasa
- Okpala ya ce kasancewar Ganduje gwamna a Kano sau biyu da kuma shugaban jam’iyya mafi girma a Afirka, muhimmancinsa a fili ya ke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani ga ikirarin jigo a NNPP, Buba Galadima cewa ba shi da amfani a siyasa
Babban mai taimaka wa Ganduje kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ta cikin sanarwar da ya fitar, ya ce Galadima sananne ne da rashin aminci a siyasa.

Asali: Twitter
A wata sanarwa da KemKem ta wallafa a shafinta na X, Ganduje ya yi mamakin yadda Galadima zai ce mutum da ya taba zama gwamna sau biyu a jiha kamar Kano, ba shi da amfani
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi Ganduje ya caccaki Buba Galadima
Jaridar Kanotimes ta ruwaito cewa shugaban APC ya ce kalaman Injiniya Buba sun nuna cewa shi mutum ne mai yaudara a siyasa.
Ya ce:
“Mun san tarihin Buba Galadima na magana barkatai, kuma ba shi da nauyi a siyasa, don haka ba mu yi mamaki da wannan ikirari mara tushe ba.”
“Ya kasance ɗaya daga cikin 'yan kungiyar Buhari, amma kullum yana ɗaukar matsayi da ya janyo gazawar ƙoƙarin kungiyar wajen samun nasarar zaɓe. Shin wannan ne mutumin da zai iya tantance wanda ke da amfani a zaɓe?”
Ganduje ya fadi muhimmancinsa a siyasa
A cikin sanarwar, Abdullahi Ganduje ya bayyana kansa a matsayin mutum da jama’a suka riga suka gwada, suka amince da shi, ɗan siyasa da masani mai maida hankali kan sakamakon zabe.

Asali: Facebook
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Shi mutum ne da ke da tabbacin nasarori a aikace da za a iya gani a fadin Kano da waje. Ayyukansa na cigaba da wanzuwa a ko’ina a Kano, abin da ke nuna dangantakarsa kai tsaye da al’umma.”
“Ganduje ɗan siyasa ne daga tushe, wanda ke da sahihan sakamako. Ina sakamakon Galadima? Shi ɗan siyasa ne marar tasiri, tsoho, kuma wanda ta kare masa a siyasa.”
“Galadima ya sani cewa jirgin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Dr. Ganduje na tafiya lafiya, kuma jam’iyyar na ci gaba da ƙarfafa ƙarfinta a ƙarƙashinsa.”
Zaɓen 2027: Makusancin Ganduje ya fadi shirinsu
A baya, kun samu labarin cewa sabon shugaban Hukumar Hadeja Jama’are, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa jihar Kano za ta mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Injiniya Rabiu Bichi ya ce yana da tabbacin cewa Kano za ta dawo jam’iyyar APC, kuma matasa za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Bola Tinubu a babban zaɓe mai zuwa.
A jawabinsa, Bichi ya caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, yana mai cewa an watsar da manyan ayyukan ci gaba da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya bari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng