'Ba Malami ko El Rufa'i ke Wakiltarmu ba,' 'Yan CPC sun fadi Jagoransu a APC
- Tsofaffin ‘yan majalisar CPC a 2011 sun nesanta kansu daga Abubakar Malami da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
- Sun ayyana Tanko Al-Makura a matsayin sahihin jagoran tsohuwar CPC, saboda haka Malami ko El-Rufa'i ba su magana da yawunsu
- Tsofaffin 'yan CPC sun tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da alƙawarin ci gaba da mara masa baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsofaffin yan majalisar wakilai ta bakwai da aka zabe su a kan dandalin tsohuwar jam’iyyar CPC sun mayar da martani kan wasu jawabai da aka alakanta da Abubakar Malami.
Malami, wanda shi ne tsohon Ministan shari'a na kasa a karkashin mulkin Muhammadu Buhari ya ce duk mai kishin kasa kuma dan asalin CPC ba ya tare da Bola Tinubu.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa a martaninsu, tsofaffin 'yan majalisar sun bayyana cewa Abubakar Malami, da tsohon gwamnan Kaduna , Nasir El-Rufa'i, ba sa magana da yawunsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan CPC sun bayyana shugabansu a APC
The Punch ta ruwaito cewa yan CPC da aka kafa APC da su, sun ce tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, shi ne jagoransu.
A jawabin bayan taro da suka yi a Abuja ranar Laraba, sun bayyana Malami da El-Rufai a matsayin ’yan siyasa marasa tasiri da daraja.
Sun ce:
“Mun lura da cewa wasu mutane da ƙungiyoyi da ba su da kima ko tasiri a lokacin da CPC ke kan ganiya, suna ƙarya suna ikirarin cewa su ke wakiltar CPC."
'Yan CPC a APC na tsaye da kafarsu
Ta bakin shugaban tsagin, Basiru Ila, sun jaddada cewa su ne ke da ikon wakiltar jam’iyyar CPC da rawar da ta taka wajen kafuwar sabuwar jam'iyya ta APC.

Asali: Facebook
Daya daga cikin wadanda suka yi taron, wanda tsohon mataimakin musamman ne ga shugaban ƙasa, Ila, ya ce:
“Mu ne wadanda aka zaɓa a jam’iyyar CPC daga majalisa ta bakwai, da sauran ’yan takara da suka tsaya takara, suka yi nasara amma aka kwace nasararsu ta hanyar da ba ta dace ba, muna nan tsaye a matsayin sahihai kuma halastattun wakilan CPC.”
Ya buƙaci ’yan Najeriya, musamman magoya bayan CPC a Arewa da sauran sassan ƙasa, da su yi watsi da duk wani bayani da ake fitarwa da sunansu.
'Yan CPC na tare da Tinubu Inji Ila
Basiru Ila ya ce su ne kadai ke da halascin kare kimar CPC, ganin irin amana da miliyoyin ‘yan Najeriya, musamman daga Arewacin ƙasar, suka ba su a wancan lokacin.
Tsofaffin wakilan sun kuma tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da alƙawarin ci gaba da kare muhimman martabar jam’iyyar APC.
Manyan CPC sun yi magana kan zaben Tinubu
A baya, mun wallafa cewa wasu jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar CPC da ta narke cikin APC sun bayyana matsayarsu a fili dangane da sake zaben Bola Tinubu a 2027.
Sun ce suna biyayya ga jam’iyyar APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, suna kara da cewa babu wani shakku a matsayar da suke da shi a siyasar Najeriya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar sun ce labaran da ke yawo cewa sun fita daga APC ko kuma sun janye goyon bayansu ga Tinubu, karya ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng