Jiga Jigan Tsohuwar Jam'iyyar Buhari, CPC Sun Fadi Matsayarsu kan Zaben 2027 da Tinubu

Jiga Jigan Tsohuwar Jam'iyyar Buhari, CPC Sun Fadi Matsayarsu kan Zaben 2027 da Tinubu

  • Tsofaffin shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC sun bayyana goyon baya ga APC da Bola Tinubu, suka ce suna nan daram cikinta
  • Sun bayyana cewa CPC na daga cikin ginshikan APC, kuma suna alfahari da rawar da suka taka wajen kafa jam’iyyar a 2015
  • Jagororin siyaasar sun karyata jita-jitan ficewarsu daga APC, suka ce hakan makirci ne na wasu don haddasa rikici a jam’iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar CPC da ta narke APC sun fadi matsayarsu game da zaben shugaban kasa a 2027.

Jiga-jigan tsohuwar mambobin CPC sun sake jaddada biyayyarsu ga jam'iyyar APC da kuma Bola Ahmed Tinubu.

Manya a tsohuwar jam'iyyar CPC sun fadi matsayarsu kan zaben 2027
Jiga-jigan tsohuwar jam'iyyar CPC sun nuna goyon baya ga Tinubu a 2027. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Matsayar ƴan tsohuwar jam'iyyar CPC a 2027

A cikin wata sanarwa da suka fitar, shugabannin CPC sun bayyana hakan a matsayin karya da makirci mara tushe, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin ‘yan CPC sun ce suna nan cikin jam’iyyar APC da cikakken goyon baya, inda suka bayyana jam’iyyar a matsayin hadin gwiwa.

Sun kara da cewa bangaren CPC ginshiki ne a cikin APC, kuma suna alfahari da irin gudunmawar da suka bayar wajen gina jam’iyyar.

Su ka ce:

“Mu da muka rattaba hannu, shugabanni ne na tsohuwar CPC, kuma mun taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC.
“Ba mu bar APC ba, kuma ba mu da niyyar barin jam’iyyar, ba za mu yarda wasu su rusa jam’iyyar da muka gina da jini da zufa ba."
Tsofaffin yan jam'iyyar CPC sun yi martani kan ficewa daga APC
Wadanda suka kafa CPC sun yi mubaya'a ga Bola Tinubu da APC. Hoto: Tinubu Media Team.
Asali: Twitter

'Yan CPC sun yabawa salon mulkin Tinubu

Shugabannin CPC sun bayyana kokarin tayar da husuma a cikin APC a matsayin mugun nufi da rarrabuwar kai da suke kin amincewa da shi.

Sanarwar ta ce:

“Muna goyon bayan sauye-sauyen tattalin arziki da mulki da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.
“Kodayake sauye-sauyen sun daurewa mutane kai, dole ne a bi su don gina tattalin arzikin kasa da kyautata makomar ‘yan Najeriya."

Sun bukaci ‘yan jam’iyya da su mara wa sauye-sauyen baya, tare da jaddada cewa korafe-korafe ba su tsaya ga bangare daya kadai ba.

Sannan sun shawarci masu korafi su bi hanyoyin da doka ta tanada a cikin jam’iyyar, maimakon su tada hankali ko ficewa cikin hanzari.

Sanarwar ta samu sa hannun manyan jiga-jigan CPC irinsu Umaru Al-Makura, Aminu Masari, Adamu Adamu da Farouk Aliyu.

Sauran da suka rattaba hannu sun hada da Lucy Ajayi, Okoi Obono-Obla da Osita Okechukwu, Premium Times ta ruwaito.

Shugaban ƙaramar hukumar Abuja ya koma APC

Kun ji cewa shugaban ƙaramar hukumar birnin Abuja da ake kira AMAC, Hon. Christopher Zakka Maikalangu ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Zakka ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin ci gaban al'ummar da yake jagoranta.

Ya ce ba shi ne ɗan siyasa na farko da ya fara sauya sheka zuwa APC ba, ya ba da misali da ɗan takarar gwamna a jihar Anambra.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.