Mace Za Ta Zama Shugabar Karamar Hukuma bayan Ciyaman Ya Rasu a Adamawa

Mace Za Ta Zama Shugabar Karamar Hukuma bayan Ciyaman Ya Rasu a Adamawa

  • Shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, Hon. Shuaibu Babas, ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya da ya dade yana yi
  • Marigayin ya taba wakiltar mazabar Fufore/Gurin a majalisar dokokin jihar da kuma zama shugaban riko na hukumar ci gaba na Malabu
  • Bayan rasuwarsa, an yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin Musulunci kamar yadda aka saba
  • Marigayin ya bar matansa, 'ya'yansa da kuma 'yan uwansa waɗanda suka yi juyayin rasuwarsa da addu'ar Allah ya jikansa da rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Fufore, Adamawa - Jihar Adamawa na cikin jimami bayan rashin shugaban karamar hukuma mai ci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban karamar hukumar Fufore, Hon. Shuaibu Babas, ya rasu.

Shugaban karamar hukuma a Adamawa ya rasu
Shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri, @AdamawaLas79384.
Asali: Facebook

An sanar da rasuwar ciyaman a Adamawa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wani mai amfani da X, @AdamawaLas79384 ya wallafa a shafinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce marigayin ya rasu ne bayan fama da wata doguwar rashin lafiya da ya dade yana yi duk da dai ba a bayyana kalar rashin lafiyar ba.

Marigayi Babas ya wakilci mazabar Fufore/Gurin a majalisar dokokin jiha, haka nan ya taba zama shugaban riko a hukumar ci gaba na Malabu.

An yi sallar jana'izar marigayin a Adamawa

Rahotanni sun ce za a yi sallar jana'izarsa gobe Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025 da misalin karfe 10:00 na safe a masallacin tsohon kasuwan Jimeta.

Marigayin ya rasu ya bar matansa, 'ya'yansa da kuma 'yan uwansa da abokan arziki.

Dukkansu sun shiga cikin jimami, suna rokon Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama.

Mace kai iya rike muƙamin shugabar karamar hukuma a Adamawa
Mace za ta iya zama shugabar karamar hukumar bayan mutuwar ciyaman a Adamawa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mace za ta iya kafa tarihi a Adamawa

Babas Shuaibu, wanda aka rantsar a matsayin shugaban karamar hukumar a watan Yulin 2024, ya rasu a yau Laraba bayan fama da wata doguwar rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Ko da yake ba a san cikakken bayani kan cutar tasa ba, wata majiya daga cikin iyalinsa ta ce:

"Ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya."

Ba a ce komai a hukumance ba tukuna, amma mutuwar Babas na iya bude kofar ga mace ta farko ta zama shugabar karamar hukuma a Jihar Adamawa.

Yaushe aka rantsar da shugabannin kananan hukumomi?

Mataimakiyar shugaban karamar hukumar Fufore, Mrs Peace Samson Audu, na daya daga cikin mata 21 da aka nada mataimaka a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar.

An rantsar da shugabannin kananan hukumomi maza 21 da mataimakansu mata 21 a shekarar 2024, cewar rahoton Daily Post.

Legit Hausa ta yi magana da yaron marigayin

Umar Abdullahi Jauro ya fadawa wakilin Legit Hausa kusancin da ke tsakaninsa da Hon. Shu'aibu Babas.

Jauro ya ce marigayin abokin mahaifinsa ne kuma asali a ƙauye daya suke.

Shi ya tabbatar da cewa za a yi jana'izarsa a gobe Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya ce:

"Abokin mahaifina ne shi kuma kauyenmu daya da shi."
Yau ne (Alhamis) za a yi janazarsa da misalin karfe 10:00 na safe a masallacin tsohon kasuwan Jimeta."

'Dan Majalisar jihar Adamawa ya rasu

A baya, mun kawo muku labarin cewa an sanar da rasuwar dan majalisa da safiyar ranar Juma'a 24 ga watan Mayun 2024 a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya.

'Dan Majalisar jihar Adamawa, Hon. Abdulmalik Jauro da ya wakilci mazabar Ganye ya rasu ne a kasar India bayan shan fama da jinya.

Kafin rasuwarsa, Jauro Musa shi ne mataimakin mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a majalisar da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.