InnalilLahi: An Shiga Jimami Yayin da Ɗan Majalisa Mai Ci Ya Rasu a Adamawa

InnalilLahi: An Shiga Jimami Yayin da Ɗan Majalisa Mai Ci Ya Rasu a Adamawa

  • Da safiyar yau Juma'a 24 ga watan Mayu aka sanar da mutuwar ɗan Majalisar jihar Adamawa, Hon. Abdulmalik Jauro
  • Marigayin da ya wakilci mazabar Ganye ya rasu ne da safiyar yau a kasar India bayan shan fama da jinya
  • Jauro Musa kafin rasuwarsa, shi ne mataimakin mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a majalisar da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - An shiga jimami bayan wani dan majalisar jihar Adamawa ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin Hon Abdulmalik Jauro Musa da ke wakiltar mazabar Ganye ya rasu da safiyar yau Juma'a 24 ga watan Mayu.

Dan majalisa mai ci ya riga mu gidan gaskiya a Adamawa
An sanar da mutuwar ɗan majalisar jihar Adamawa, Hon. Abdulmalik Jauro Musa. Hoto: Abdulmalik Jauro Musa.
Asali: Facebook

Adamawa: Marigayin ya rasu kasar India

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

The Nation ta tattaro cewa marigayin wanda ɗan jam'iyyar APC ne ya rasu a kasar India bayan fama da jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jauro Musa shi ne mataimakin mai tsawatarwa na marasa rinjaye a majalisar da ke cike da mambobin jam'iyyar PDP mai mulki jihar, Daily Post ta tattaro.

Wani daga cikin abokan mamacin, Abdurasheed Takai ya nuna alhinin rasuwar Jauro Musa inda ya yi masa addu'ar samun rahama.

"Allah ya sa mutuwa ta zama hutu a gare ka, Hon. Abdulmalik Jauro Musa."

- Abdulrashid Takai

APC a Adamawa ta aiko ta'aziyya

Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a jihar, Mohammed Abdullahi ya nuna alhini kan mutuwar marigayin.

Abdullahi ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma Majalisar jihar kan wannan babban rashi da aka yi.

"Cikin alhini muke tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi da iyalansa da kuma mambobin majalisar jihar."

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure da aka bindige ɗan sanda a tsakiyar kasuwar Jos

"Muna kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki da kuma yan jam'iyyar APC da ke karamar hukumar Ganye."

- Mohammed Abdullahi

'Dan majalisar Kano ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan majalisar jihar Kano, Halilu Kundila ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 59 a duniya.

Marigayin wanda ɗan jami'yyar APC ne ya rasu a ranar Asabar 6 ga watan Afrilu bayan fama da jinya.

Marigayin ya raba kayan tallafi ga al'ummar mazaɓarsa domin rage musu radadi mako daya kafin Allah ya dauki ransa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel