Magana Ta kare: Shugabannin APC Sun Fadi Gwamnan PDP da Zai Koma Jam'iyyarsu

Magana Ta kare: Shugabannin APC Sun Fadi Gwamnan PDP da Zai Koma Jam'iyyarsu

  • Ana ci gaba da magana kan batun komawar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa jam'iyyar APC
  • Shugabannin APC na ƙabilar Ijaw a jihar Delta sun tabbatar da cewa gwamnan na PDP zai koma jam'iyyarsu a kowane lokaci
  • Sun kuma nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio
  • Shugabannin na APC sun ba da tabbacin cewa suna maraba da duk wani mai son shigowa jam'iyyar da ke mulki tun 2015

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Shugabannin jam’iyyar APC na ƙabilar Ijaw a jihar Delta sun tabbatar da cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, zai shiga jam’iyyarsu a kowane lokaci.

Sun kuma kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasu shugabannin jam’iyyar.

Gwamna Oborevwori zai koma APC
Shugabannin APC sun ce Gwamna Sheriff Oborevwori zai koma jam'iyyar Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce shugabannin na APC ƙarƙashin jagorancin Michael Johnny, sun tabbatar da hakan ne a wani taron shugabannin APC na Ijaw da aka gudanar a Effurun, ƙaramar hukumar Uvwie a jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sheriff Oborevwori zai koma APC

Michael Jonny ya tabbatar da cewa Gwamna Sheriff Oborevwori zai shigo jam'iyyar APC.

"Gwamna Sheriff Oborevwori zai shigo APC. Ku manta da abin da kuke ji a kafafen sada zumunta. Sheriff Oborevwori zai shigo APC."
"A matsayinmu na mutanen ƙabilar Ijaw, ba mu da matsala da wanda ke son shigowa APC."

- Michael Jonnƴ

Ya ƙara da cewa kowane mutumin Ijaw da ke son shiga jam’iyyar yana da ƴancin yin hakan.

Michael Johnny ya bayyana cewa ana ci gaba da sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP a ɓangaren Ijaw na Delta ta Kudu zuwa APC.

A wajen taron akwai Raymos Guana, Mike Seikegba, Joe Ekiyor, Sir Theodore Ezonfade, Chief Davi Omare, Hon. Ebitonmo A. Alapala, Cif Promise Lawuru, Hon. Wurus Fortune, Hon. Joseph Izonowei Sozaowei, Blackman Edisemi Mule, da sauransu.

Michael Johnny ya ce babu wata matsala ta shugabanci a tsakanin shugabannin APC na Ijaw a jihar Delta.

Shugabannin sun nuna goyon baya ga Tinubu

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya samu goyon baya a Delta Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jigon na APC ya yi alƙawarin ci gaba da goyon baya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

“Muna biyayya ga kwamitocin gudanarwa na jiha da na ƙasa na APC, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Godswill Akpabio."

- Michael Jonny

Michael Johnny ya godewa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da ya bai wa mutanen yankin Delta ta Kudu, inda ya bayyana cewa ya ba da muƙamai ga kusan mutane uku daga yankin.

Jiga-jigan APC ba sa maraba da Gwamna Sheriff

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Delta sun bayyana cewa ba sa maraba da shigowar Gwamna Sheriff Oborevwori.

Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa ko kaɗan ba sa gayyatar Gwamna Sheriff Obororevwori na PDP domin shigowa jam'iyyar.

Ned Nwoko ya tabbatarwa da gwamnan cewa jam'iyyar APC za ta karɓe mulkin jihar daga hanun PDP a babban zaɓe na shekarar 2027 mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng