Wike Ya Gindaya Sharuɗan Yafewa Gwamna Fubara Laifuffukan da Ya Yi
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yafe wa gwamna Fubara ne kaɗai idan ya nemi gafara ta gaskiya
- Rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara yana da nasaba da mulki da ikon albarkatu a jihar Rivers da majalisar dokokin jihar
- Wike ya ce gwamnoni biyu sun roƙe shi ya sasanta da Fubara, inda ya amsa cewa yana shirye matuƙa idan akwai gaskiya
- Ya ce shugaban ƙasa Tinubu ya ceci jihar daga rikici, duk da cewa shi kansa yana so a tube Gwamna Fubara gaba ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rikicin siyasar Rivers ya sake daukar sabon salo musamman tsakanin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana sharadin yafewa dakataccen Gwamnan jihar Ribas watau Siminalayi Fubara.

Asali: Facebook
Wike ya buƙaci neman yafiya daga Fubara
Wike ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da aka yi ranar Juma’a a birnin Abuja, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan jihar, ya ce zai yafe wa Fubara idan har ya nemi afuwa da zuciya ɗaya da gaskiya.
Lokacin da aka tambaye shi ko zai yafe wa Fubara idan ya nemi gafara, Wike ya ce:
“Idan har ya nemi gafara ta gaskiya ba.”
A 'yan kwanakin nan, dangantaka tsakanin Wike da Fubara ta yi tsami, rikici ya barke tsakaninsu saboda neman iko a jihar.
Sabani tsakaninsu ya samo asali ne daga kokarin neman iko kan tattalin arzikin jihar da kuma ɓangaren siyasa.

Asali: Facebook
Wike ya magantu kan sulhu da Fubara
A yayin hirar, Wike ya bayyana cewa wasu gwamnoni biyu sun nemi ganinsa domin sulhunta rikicin da ke tsakaninsa da Fubara, cewar Punch.
Ko da yake bai ambaci sunayen gwamnonin ba, Wike ya ce ya shaida musu cewa ya yanke shawarar samun zaman lafiya da magajinsa.
Ya ce:
“Wannan gwamnoni biyu sun zo wurina, na ce, kalli, ina nan don zaman lafiya. Me yake so?’ Suka ce, ‘Za mu yi komai'.
“Da gaskiya, idan wani zai zo, dole ya zo da gaskiya. Lokaci mafi dacewa shi ne lokacin da shugaban ƙasa ya shiga tsakani."
Ministan ya kuma goyi bayan matakin shugaban ƙasa Bola Tinubu na ayyana dokar ta baci a Rivers, yana mai cewa yana son a tube Gwamna Fubara.
Amma Wike ya ce wannan matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka ne ya ceci jihar Rivers daga rugujewa, kuma naɗa shugaba guda abu ne mai kyau.
Ibas ya magantu kan zancen tuhumar Fubara
Kun ji cewa shugaban riƙon ƙwarya na jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas ya ƙaryata rahotanni cewa zai binciki dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara da Ngozi Odu.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, an buƙaci jama'a da su yi watsi da rahotannin da suka fara karade gari.
Gwamnatin jihar ta ce rahoton bai da tushe kuma ƙarya ce da masu neman tayar da hankali ke amfani da ita domin tada zaune tsaye a jihar da ta sha fama da rigima.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng