Tinubu zai Dauki Matakin Gaggawa kan Tsaro bayan Dawowa daga Faransa
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da hafsoshin sojoji da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu bayan dawowar shi Najeriya
- Tun daga ranar 2 ga Afrilu da ya tafi Paris, akalla mutane 120 aka kashe a hare-haren ‘yan bindiga, tare da kona gidaje da raba dubban mutane da muhallansu
- Fadar Shugaban kasa ta zargi gwamnonin jihohi da gazawa wajen amfani da kudin tsaro da suke karba, tace hakan na kara haddasa tabarbarewar tsaro
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida daga tafiyar aikin makonni biyu zuwa kasashen Turai.
Rahotanni sun nuna cewa Tinubu ya shirya taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro domin duba halin da ake ciki a wasu jihohin kasar.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa Tinubu ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Abuja da misalin karfe 9:50 na dare a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai gana da hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu ya samu rahotanni masu tayar da hankali daga lokacin da ya tafi hutu, inda aka hallaka fiye da mutane 120 a hare hare a jihohi.
A cewar majiyoyi daga fadar shugaban kasa, Shugaban Tinubu zai gana da hafsoshin tsaro da ministoci domin duba yadda za a magance matsalar, musamman a Filato, Benue da Borno.
An kashe fiye da mutane 50 a Benue
A jihar Benue, akalla mutane 56 ne suka rasa rayukansu a hare-hare biyu da aka kai wa al’umman Logo da Gbagir.
Rahotanni sun nuna cewa an kona gidaje da dama, inda kusan mutane 3,000 suka rasa matsugunansu duk da kasancewar jami'an tsaro a yankin.
Fadar shugaban kasa ta zargi gwamnoni
Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya zargi wasu gwamnoni da rashin amfani da kudin tsaro yadda ya kamata, duk da cewa suna karɓar makudan kudi duk wata.
A cewarsa:
“Wasu gwamnoni na bai wa jami'an SSS, ‘yan sanda da sojoji N20m a wata, amma kudin tsaron da suke karba ya kai N1bn zuwa N3bn. To ina sauran kudin suke?”
Ya kara da cewa, maimakon jiran kafa ‘yan sandan jihohi, gwamnoni na iya amfani da abin da suke da shi domin karfafa tsaro, ta hanyar samar da kayan aiki da goyon bayan jami’an tsaro.
Bwala ya bukaci gwamnoni su kafa rundunonin tsaron yankuna a matakin kananan hukumomi da gundumomi domin tattara bayanan sirri da dakile hare-haren da suka zama ruwan dare.

Asali: Facebook
Rahoton Channels TV ya nuna cewa tsohon ministan tsaro, TY Danjuma ya yi kira da cewa ya kamata 'yan Najeriya su fara kare kansu, lamarin da gwamna Umar Namadi ya soka.
Tinubu ya yi kira ga al'ummar Musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su nuna gaskiya, adalci da tausayi.
Bola Tinubu ya ce ana lokacin da ya kamata Musulmai su hada kai da sauran mutanen duniya domin kawo zaman lafiya da cigaba.
Legit ta rahoto cewa Tinubu ya yi kiran ne a wani taron Musulunci a Ogun da mataimakiyar gwamnan jihar ta wakilce shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng