2027: Kwankwaso Ya Caccaki Hakeem Baba Ahmed, Buba Galadima kan Sukar Tinubu
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi martani kan sukar gwamnatin Bola Tinubu da Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima suke yi
- Jigon na jam'iyyar APC a jihar Kano, ya ce mutanen biyu ba su isa su hana a sake zaɓen shugaban ƙasan ba a shekarar 2027
- Hon. Musa Kwankwaso ya nuna cewa yankin Arewa ba zai juyawa Tinubu baya ba, domin ya kawo masa ayyukan ci gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja da Jama’are, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya caccaki Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima ba su da ƙarfin hana Shugaba Bola Tinubu sake lashe zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta rahoto cewa jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima sun kasance cikin masu sukar manufofin Bola Tinubu a ƴan kwanakin nan.
Musa Kwankwaso ya caccaki masu sukar Tinubu
A martaninsa kan sukar da suke yi, Kwankwaso ya ce mutanen biyu ba su da halin ƙwarai da zai sa su zargi gwamnatin Tinubu, inda ya buƙaci ƴan Najeriya ka da su dauke su da muhimmanci.
"Hakeem Baba-Ahmed ya ƙarbi muƙami a gwamnatin Tinubu yana tunanin kamar yadda ake yi a baya ne, inda masu muƙami ke rayuwa cikin jin dadi ba tare da aiki ba."
“Da ya fahimci cewa wannan gwamnati ta sha banban, ya gane bai dace da wurin ba, sai ya gudu. Yanzu Hakeem Baba-Ahmed ba zai iya faɗin dalilin da ya sa ya karɓi aikin ba, da kuma dalilin da ya sa ya ajiye shi."
“Yanzu ya koma cikin kwanciyar hankali yana tunzura jama'a kan gwamnatin da ya taɓa yi wa aiki. Ya kamata ya fito fili ya gaya wa ƴan Arewa gaskiya game da abinda ya aikata."
- Musa Iliyasu Kwankwaso
Kwankwaso ya caccaki Buba Galadima
Kwankwaso ya ƙara da cewa Buba Galadima ko rumfar zaɓe ɗaya ba zai iya lashewa ba.

Asali: Twitter
“Dukkanin shekarun da ya yi tare da Janar Buhari, me ya kawo masa? Maimakon haka, Buhari ya samu nasarar lashe zaɓuɓɓukansa ne bayan irinsu Buba Galadima sun bar shi."
“A gefe guda kuma, Bola Tinubu cikin ƙasa da shekaru biyu kacal na mulkinsa, ya kawo ci gaba mai yawa zuwa Arewa, duba titin Kano zuwa Abuja, duba hanyar Badagry zuwa Kebbi."
"Bari na tabbatarwa da Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima cewa Bola Tinubu zai lashe wa’adin mulki na biyu tare da goyon bayan Arewa, domin ƴan Najeriya sun yaba da manufofin da shugaban ƙasa ke aiwatarwa."
- Musa Iliyasu Kwankwaso
Jigo a SDP ya gargaɗi El-Rufai kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ja kunnen Nasir Ahmed El-Rufai.
Adebayo ya bayyana cewa ba za su bari a ƙwace jam'iyyar ba domin yin yaƙi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewa jam'iyyar SDP ba za ta shiga faɗan da babu ruwanta ba, inda ya buƙaci masu fushi da Tinuɓu da su je can su warware matsalar da ke tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng