‘Yar Hassada ce’: Musa Kwankwaso Ya Soki Naja’atu, Ya Jero Manyan da Ta Zaga

‘Yar Hassada ce’: Musa Kwankwaso Ya Soki Naja’atu, Ya Jero Manyan da Ta Zaga

  • Jigon APC, Musa Ilyasu Kwankwaso ya soki Naja'atu Muhammad, yana zarginta da cin mutuncin manyan ‘yan siyasa da shugabannin Najeriya
  • Ya ce tun zamanin Obasanjo har zuwa Jonathan da Atiku, Naja'atu ta saba da sukar shugabanni da maganganu marasa dadi da kuma cin mutunci
  • Kwankwaso ya bukaci Naja'atu da ta je kotu idan ana zargin ta da keta doka, maimakon ci gaba da sukar da ba tushe musamman bayan zargin Ribadu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya soki yar gwagwarmaya Naja'atu Muhammad kan zarge-zargenta.

Ilyasu Kwankwaso ya bayyana Naja'atu da yar hassada inda ya ce ta zagi manyan yan siyasa da tsofaffin shugabannin Najeriya.

Kwankwaso ya caccaki Naja'atu kan kalamanta
Musa Ilyasu Kwankwaso ya fadi irin munanan halayen Naja'atu Muhammad tun a shekarun baya. Hoto: Musa Ilyasu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Kwankwaso ya caccaki Naja'atu kan zarge-zargenta

Tsohon kwamishinan a Kano ya bayyana haka ne a bidiyo yayin hira da DCL Hausa da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Kwankwaso ya jero tsofaffin shugabannin Najeriya da kuma manyan yan siyasa da Naja'atu ta ci mutuncinsu.

Ya ce tun lokacin Olusegun Obasanjo ta zage shi haka ta zagi Goodluck Jonathan da gwamnatin Abdulsalam Abubakar da kuma Atiku Abubakar.

Kwankwaso ya fadi gwagwarmayar Naja'atu ga Buhari

"Ina son aika sako ga Naja, tun da ta kai shekaru 67 zuwa 70 a duniya, na dauka za ta taimaki matasa sai kawai ta koma adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
"Amma tun a baya, ta saba da cin mutuncin mutane da cewa jami'an tsaro karnuka na nemanta, ya kamata ta je kotu ta ba da amsa kan abin da take fada.
"Lokacin da kowa ke son Buhari, za a zabe shi, da ita da Buba Galadima sun fi kowa cin mutuncin mutane kowa ya sani, sai da suka bar jikin Buhari sannan ya yi nasarar hawa mulki."

- Musa Ilyasu Kwankwaso

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu

Jigon APC ya fadi matsalolin Kwankwaso

Mun ba ku labarin cewa jigon APC a Kano, Musa Ilyasu Kwanwkaso ya gargadi shugabannin jam'iyyar da su yi taka tsan-tsan kan shirin shigowar Rabiu Kwankwaso.

Musa Ilyasu ya zargi Sanata Kwankwaso da kokarin amfani da APC ne kawai domin tabbatar da wa’adin Abba Kabir Yusuf a 2027, ba don amfanin jam’iyyar ba.

'Dan siyasar wanda babba ne a APC ya bukaci Tinubu da ya yi nazari kan tarihin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa ya saba cin amana a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.