Kwankwaso Ya Soki Martanin Gwamnatin Abba bayan Kisan Mutum 4 wajen Rusau
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki gwamnatin Kano a kan matakin da ta dauka bayan kashe wasu mazauna karamar hukumar Ungogo
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce an kafa kwamitin bincike kan kisan mutane hudu da aka yi yayin aikin rusau a unguwar Rimin Zakara
- Amma Honarabul Kwankwaso ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci iyalan mamatan domin yin ta’aziyya tare da ba da diyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jagora a jam’iyyar APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya soki shirin gwamnatin Jihar Kano na kafa kwamitin bincike kan kisan mutane hudu a jihar
A daren Lahadi ne aka samu rahoton cewa an kashe mutanen ne yayin wani aikin rusau da aka gudanar a Rimin Zakara, karamar hukumar Ungogo a jihar.

Kara karanta wannan
"Ba za su iya ba": Gwamna ya sallami hadimai 2 mata daga aiki, ya umarci su bar ofis

Asali: Facebook
Mai taimaka wa Musa Kwankwaso a harkokin yada labarai, Musa Dan Zaria, ya tabbatar wa da Legit cewa ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin da ya dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ya kamata gwamnan tare da kwamishinansa na filaye da ayyuka su ziyarci iyalan wadanda abin ya shafa domin yin ta’aziyya.
Musa Kwankwaso ya shawarci Gwamnatin Kano
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Musa Illiyasu Kwankwaso na ganin irin wannan tuntuba da kai-tsaye na da muhimmanci wajen magance rikicin da sanyaya wa jama'a.
Ya bukaci gwamnati da ta biya diyya ga iyalan mamatan tare da ware masu sabbin filaye ga wadanda aka rushe gidajensu.
Ya ce:
"Inkarin da gwamnati ke yi cewa ba ta da hannu a aikin rusau din maganar banza ce."
"Yawancin gidajen rediyon cikin gida sun ruwaito cewa jami’an ma’aikatar filaye sun kasance tare da jami’an tsaro yayin aikin rusau din."
“Abba ba shi da iko a Kano” Hon. Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan
Kusa a APC ya fadi abin da zai faru idan Kwankwaso ya dawo jam'iyya, ya gargadi Tinubu
Musa Illiyasu Kwankwaso ya kara da zargin cewa aikin rusau din ya nuna rashin ikon shugabanci a gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Ya zargi cewa shugaban jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ne ke jagorantar gwamnatin ta hannun Abba Gida Gida.
Hon. Kwankwaso ya ce:
"Ya kamata mutanen Kano su gane su waye makyansu. Gwamnatin NNPP a Kano ba za ta kawo komai ba sai wahala, rasa rayuka, da lalacewar dukiyoyi, kamar yadda ya faru a Rimin Zakara."
Ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya jawo wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi rashin nasara a zaben 2027.
Kano: An banka wa gidan basarake wuta
A baya, mun ruwaito cewa , mazauna Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungogo sun fada a cikin dimuwa bayan an harbe mutane hudu yayin da su ka yi arangama da masu rushe-rushe.
Tashin hankalin ya samo asali ne daga wani yunkuri da jami’an gwamnatin Kano su ka yi na rushe gine-gine da ake zargin an gina su ba bisa ƙa’ida ba da ake zargin mallakin jami'ar BUK ne.
Rikicin ya yi ƙamari lokacin da jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zangar, lamarin da ya haifar da arangama da harbe-harbe har aka kashe mutum hudu da jikkata wasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng