Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

  • Fastocin takarar shugabancin kasa na Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi sun bazu a titunan Kano
  • Mutanen gari sun farko ranar Lahadi ne sun ga fastocin a manyan tituna da fitattun wurare a birnin
  • Wata kungiyar matasa masu kishin ƙasa magoya bayan Gwamna Bala Mohammed ne suka ɗauki nauyin yin fastocin

Mazauna birnin Kano sun farko a ranar Lahadi sun ga fastocin gwamnan jihar Bauchi, an liƙa su a manyan tituna a cikin birnin, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan shine na baya-baya cikin jerin fastocin takarar shugaban ƙasa da ake liƙawa a jihar ta Kano.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Wuraren da aka ga fastocin

Daily Trust ta ruwaito cewa an gano fastocin a Fly Over na Zaria road, Gadar Lado, Club road, Zoo road, Shataletalen Dangi, Court road da wasu wurare a birnin na Kano.

Idan za a iya tunawa, fastocin jigon jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu; tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu na daga cikin wadanda aka gani a titunan tsohon birnin mai ɗimbin tarihi.

KU KARANTA: Buhari ya yi martani kan barazanar da Niger Delta Avengers ta yi na gurgunta tattalin arzikin Nigeria

Fastocin da ƙungiyar matasa masu kishin ƙasa na Bala Mohammed 2023 suka ɗauki nauyi na ɗauke da rubutu mai cewa: To move Nigeria foward 2023'.

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin daban, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Malam Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel