Shettima, Gwamnoni, Ministoci Sun Dura Bauchi Nadin Sarautar Tsohon Gwamna
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnoni da wasu manyan jami’an gwamnati zuwa Bauchi domin halartar nadin sarauta
- Tsohon gwamnan Bauchi ya samu sarautar Makama Babba daga fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, yayin da aka hada bikin da daurin auren diyarsa
- Bala Mohammed ya yaba da gudummawar tsohon gwamnan tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyukan raya kasa musamman a karkara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Birnin Bauchi ya cika da baki daga sassa daban-daban na kasar nan yayin da aka gudanar da nadin sarauta ga tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar.
Rahotanni sun nuna cewa an yi bikin nada Mohammed Abubakar a matsayin Makama Babba na masarautar Bauchi.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya kuma kunshi daurin auren diyarsa, Khadija Mohammed, wanda aka yi a fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu.
Bikin ya ja hankalin fitattun mutane ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban gwamnonin Arewa, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Haka zalika, ministoci, ‘yan majalisa da manyan ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban na kasar nan sun halarci bikin domin nuna goyon baya da girmamawa ga tsohon gwamnan.
An yaba da ayyukan tsohon gwamnan
A yayin jawabin da ya gabatar, Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu, ya ce an ba Mohammed A. Abubakar sarautar ne saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.
Mai martaba Rilwanu Suleiman Adamu ya ce tsohon gwamnan ya bayar da gudumawa tun daga lokacin da ya fara rike mukaman gwamnati.
Ya bukace shi da kada ya yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da taimakawa jama’ar jihar, yana mai cewa sarauta tamkar nauyi ce da ake bukatar jajircewa da kishin kasa wajen tafiyar da ita.

Asali: Facebook
Gwamna Bala ya jaddada kudirin raya karkara
A nasa bangaren, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da ayyuka masu amfani ga jama’a a duk fadin jihar, musamman a karkara.
Daily Trust ta wallafa cewa Bala Mohammed ya ce:
“Mun kuduri aniyar gina hanyoyi, samar da ruwa da inganta rayuwar jama’a, musamman a yankunan da ba su da isasshen ci gaba.
"Wannan nadin sarauta alama ce ta hadin kai da girmamawa.”
Bala Mohammed ya kuma yi fatan sabon Makama Babba zai ci gaba da taka rawa a kokarin hadin gwiwa don kawo ci gaba da zaman lafiya a jihar Bauchi da ma kasa baki daya.
Gwamnan Bala ya ziyarci iyalan Dutsen Tanshi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ziyarci mutanen Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa Dr Idris tare da cewa malamin ya bayar da gudumawa sosai.
Baya ga haka, Bala Mohammed ya yi alkawarin mika filin Idin Games Village ga daliban Dr Idris domin cigaba da yin ibada a wajen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng