Ana Batun Hadaka, Wike Ya Kwancewa PDP Zani a Kasuwa kan Zaben 2027

Ana Batun Hadaka, Wike Ya Kwancewa PDP Zani a Kasuwa kan Zaben 2027

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya taɓo batun haramar jam'iyyar PDP kan babban zaɓen 2027
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa jam'iyyarsa watau PDP ba ta shirya tunkarar babban zaɓen na shekarar 2027 ba
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya nuna cewa PDP ba ta tsarin da za ta iya ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan shirin jam'iyyar PDP domin zaɓen 2023.

Nyesom Wike ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta shirya tunkarar zaɓen gama-gari na shekarar 2027 ba.

Wike ya caccaki PDP
Wike ya ce PDP ba ta shirya ba don zaben 2027 Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta kai-tsaye da manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, 18 ha watan Afirilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya danganta rashin shirin na PDP kan rashin ingantaccen tsarin da zai iya ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Wike: 'PDP ba ta shirya ba kan zaɓen 2027'

Wike ya soki yadda jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta na cikin gida, tare da bayyana shakku game da shirinta don zaɓe mai zuwa.

“PDP ba ta shirya don zaɓen 2027 ba. Wannan abu ne da ke a bayyane. Misali, ina da jarabawa kuma na tafi aji domin yin karatu. Amma shin da gaske ina yin karatun kuwa? Shin ina yin nazari?"
“Ba sai ka yaudari kowa ba ka nuna kana karatu. Kana ƙoƙarin nuna cewa kana karatu ne kawai domin mutane su ga ka ɗauki jakarka ka shiga aji."
“Wannan shi ne halin da PDP ke ciki. Don haka ba za su iya ba da tabbacin cewa sun shirya don 2027 ba. Rikicin neman mulki ba zai taimaki jam’iyyar ba."

- Nyesom Wike

Wike ya daɗe yana sukar jam'iyyar PDP

Nyesom Wike
Wike ya dade yana addabar PDP Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne kuma ɗaya daga cikin shugabannin G5 waɗanda su ke adawa da jagorancin PDP, ya shahara wajen sukar PDP.

'Dan siyasar ya saba kaca-kaca da shugabancin jam’iyyar da kuma yadda take tafiya, musamman gabanin zaɓen shekarar 2023.

Tasirinsa ya ci gaba da haifar da muhawara dangane da haɗin kai a cikin jam’iyyar da dabarun ƴan adawa.

Maganganunsa sun zo ne a daidai lokacin da shugabannin ƴan adawa a faɗin ƙasar nan ke ƙoƙarin haɗaka don fuskantar APC a babban zaɓen 2027.

Sai dai, wannan tattaunawa ta haɗaka na fuskantar cikas saboda saɓanin ra’ayoyi tsakanin manyan masu ruwa da tsaki.

Wike ya so a tsige Gwamna Simi Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya so a ce an tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Ministan ya bayyana cewa bai ji daɗin sanya dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya ba a jihar Rivers.

Wike ya nuna cewa da ba a sanya dokar ta ɓaci a jihar ba, da tuni ƴan majalisar dokoki sun tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng