Farfesa Yusuf Ya Tona Yadda Tsohon AGF Ya 'Ƙwamushe' Naira Biliyan 10 a Mulkin Buhari
- Tsohon Shugaban NHIS, Usman Yusuf ya fallasa yadda tsohon Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya cire N10bn daga asusun NSA
- Farfesa Usman Yusuf ya ce tsohon Akanta ya cire waɗannan kudi ne a lokuta biyu watau Naira biiyan 5 sau biyu kuma ba tare da izini ba
- Ya ce ya yi kokarin bin kadin kudin ta hanyar neman zama da ministar kuɗi amma abin ya ci tura duk da sa bakin sakataren gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya fallasa wata badaƙalar tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris.
Farfesa Yusuf ya ce Ahmed Idris, ya cire Naira biliyan 10 daga asusun bai ɗaya (TSA) na hukumar ba tare da amincewarsa ba a matsayinsa na shugaban NHIS.

Asali: Facebook
Farfesa Yusuf ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis mai taken: “Tsayawa kan gaskiya komai runtsi," kamar yadda Sahara Reporters ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Yusuf ya kwato sama da N100bn
Ya ce an cire waɗannan makudan kudi a lokacin da yake ƙoƙarin dawo da fiye da Naira biliyan 100 na kudin NHIS da ke makale a wasu bankuna 13.
A cewarsa, bankunan sun ki yarda su tura kuɗin zuwa asusun TSA wanda ya saɓa wa umarnin Gwamnatin Tarayya wacce ta maida amfani da asusu guda ɗaya tal.
Yusuf ya kara da cewa ya dauki wani kamfanin aiki a lokacin domin ya gudanar da bincike kan harkokin kudi na hukumar NHIS.
Ya ce rahoton binciken ya bayyana cewa bankuna 13 sun ki yarda su tura kudin da suka haura Naira biliyan 100 zuwa asusun TSA.
Farfesa Usman Yusuf ya ce manyan jami’an gwamnati da ya nemi taimako wajen dawo da wadannan kudade sun ki ba shi goyon baya a wannan lokacin.
Ya ce wadanda ya tuntuba sun hada da tsohon ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole, gwamnan CBN a lokacin, Godwin Emefiele; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari, da Antoni Janar na Tarayya.
Yadda tsohon AGF ya cire N10bn daga TSA
Tsohon shugaban NHIS ya ce:
“Duk da kokarina na neman taimako daga manyan jami’an gwamnati, ba wanda ya taimaka.
"A karshe kuma, Akanta Janar ya cire Naira biliyan 10 a lokaci biyu (Naira biliyan 5 sau biyu) daga asusun NHIS-TSA ba tare da shawara ko izini na ba a matsayina na Shugaban Hukumar.”

Asali: Twitter
Wane mataki shugaban NHIS ya ɗauka?
Yusuf ya ce sau da dama ya aika takarda ga Ministar Kudi na lokacin, Kemi Adeosun, don ganawa da ita kan cire kudin ba bisa ka’ida ba, amma ta ki ganinsa.
Ya kara da cewa:
“Na kai kokena ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya B.D. Lawal, wanda ya kira ta a gabana ya umurce ta ta gan ni, amma ta ki, har zuwa lokacin da ta bar gwamnati.”
EFCC ta maka Akantan Bauchi a kotu
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta maka Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja a gaban kotun kan zargin karkatar da N8.3bn.
Sirajo Jaja ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ne tare da wani ɗan canji da kamfaninsa mai suna Jasfad Resources Enterprise.
Ana kuma zarginsu da karkatar da kuɗin gwamnati da kuma almundahanar kuɗi da darajarsu ta kai N8,380,626,430.95.
Asali: Legit.ng