"Za Mu Dawo da Mulkin Adalci a Najeriya," Atiku Ya Fadi Yadda Hadakarsa za Ta Rusa Tinubu
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa kawancen da suke jagoranta zai rungumi kowacce hanyar kawo shugabanci nagari a Najeriya kafin zaben 2027
- Ya ce "jirgin kawance" ya fara tafiya kuma zai tsaya a wurare da dama domin karbar ‘yan Najeriya masu ra'ayin ci gaba daga kowane bangare
- Atiku ya shawarci matasa da kada su sayar da makomarsu saboda wasu ‘yan kudi da za a basu, wanda ba zai amfana wa rayuwar komai ba
- Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce an samar da kawancen jam’iyyun ne domin ceto yan Najeriya daga mulkin gwamnatin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fadi yadda kawancen ‘yan adawa za ta kai ga ci.
Ya bayyana cewa za su rungumi kowane dandali da zai tabbatar da manufarsu ta kyakkyawan shugabanci domin kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027

Asali: Facebook
A wani bidiyon taron da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, Atiku ya tabbatar da cewa jirgin kawancen jam'iyyu ya bar tasha, kuma zai tsaya a wurare da dama domin daukar ‘yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ne ya bayyana hakan ne yayin wani taro da wata tawaga ta National Opinion Leaders, kwana biyu bayan Kungiyar Gwamnonin PDP ta nesanta kanta da hadakar jam'iyyunsa.
Shawarar Atiku ga matasa kan zaben 2027
Daily Trust ta wallafa cewa a yayin da yake jawabi ga tawagar National Opinion Leaders da yawansu matasa ne, Atiku ya bukace su da su gujdewa ruɗin kyautar kudin da bai taka kara ya karya ba.
Ya ce:
“Kada ku bari a ruɗe ku da wasu kudade kaɗan da ake bayarwa, har ku yarda ku sayar da makomarku da makomar ‘ya’yanku.”
“Saboda haka ne wasu daga cikinmu shugabanni daga jam’iyyun da na ambata – APC, PDP, LP da sauransu – mu ka yanke shawarar cewa za mu samar da abinda nake kira da Hausa ‘Sabuwar tafiya’, wato a Turance, a new path – wata sabuwar hanya zuwa sabuwar Najeriya.”
“Mun fara ganawa, kuma da ikon Allah, ba da jimawa ba za mu bayyana wannan sabuwar tafiya, muna kuma fatan ku matasa ku kasance a cikinta.”
Atiku ya fadi manufar kawancen jam’iyyu
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce babban burin wannan kawance shi ne samar da shugabanci nagari.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Duk wata hanya da za ta ba mu damar samun kyakkyawan shugabanci don makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu, to wannan ce hanyar da za mu bi.”
“Ku fara tsara yadda za ku hada kai, ku kuma fara aiki tare domin samun karin ‘yan Najeriya da za su rungumi wannan sabuwar tafiya.”
Tinubu: Atiku ya soki gwamnonin PDP
A baya, kun samu labarin cewa hadakar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta ta bayyana fushinta a kan gwamnonin jam’iyyar PDP.
Gwamnonin sun fitar da matsayarsu a kan batun kawancen jam'iyyu, wacce ke neman kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, amma abin bai yi wa hadakar dadi ba.
Kawancen jam'iyyun ya zargi gwamnonin PDP da kokarin dakile muryar 'yan adawa, wanda hakan zai ba APC damar ci gaba da mulki a kasar nan har bayan zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng