2027: Buba Galadima Ya Fadi Abin da zai Sanya a Samu Sahihin Zabe a Najeriya
- Jigo a jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya, Buba Galadima ya yi tsokaci kan babbam zaɓen shekarar 2027
- Buba Galadima ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su tashi domin ganin an gudanar da sahihin zabe a lokacin
- Ya nuna cewa za a samu hakan ne kawai idan ƴan Najeriya sun jajirce wajen ganin cewa an yi wa dokar zaɓe gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban ƙusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi magana kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe nan gaba.
Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa ƙuri'u ba za su yi amfani ba a lokacin zaɓen gama-gari na 2027.

Asali: Facebook
Babban ƙusan na NNPP ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Buba Galadima ya ce kan zaɓen 2027?
Buba Galadima ya nuna cewa ƙuri'u ba za su yi amfani ba a zaɓen idan har ƴan Najeriya ba su tashi tsaye domin neman a yi wa dokar zaɓe gyara ba.
Ya ce ƴan Najeriya su manta da batun zaɓen 2027 kawai idan har ba su tashi an yi wa dokar zaɓen gyara ba.
"Dole ne mu haɗa kai mu tabbatar mun samu ingantacciyar dokar zaɓe da za ta tabbatar da cewa ƙuri'ar kowa da kowa tana da mahimmanci. Wannan shi ne abu guda tilo da za mu iya yi."
"Idan ba za mu iya yin hakan ba, to mu manta kawai, domin idan ƴan Najeriya ba su haɗa kai ba, wasu za su ci gaba da rubuta sakamakon zaɓe da kansu."
"Yadda al’amura ke tafiya a halin yanzu, ƙuri’u ba sa amfani a wajen zaɓe a Najeriya."
"Idan ba mu gyara dokar zaɓe ba, kotuna za su ci gaba da ba su komai, kamar yadda suka yi a Edo. Wani ya ci zaɓe, amma aka ba wani sakamakon, kuma kotu ta tabbatar da hakan."
- Buba Galadima
Buba Galadima ya koka da ƙarfa-ƙarfan da ake yi

Asali: Twitter
“Ka duba abin da ya faru a Kano. Kowa ya san cewa aikin gwamna ne ya amince da naɗin sarki. Ba shi ke naɗa sarki ba, sai dai ya amince ko ya ba da shawara."
"Amma wani na son naɗa sarki daga Abuja, kuma babu wanda ke magana. To, me zai sa in ɓata lokacina ina magana?"
"Ka duba abin da ke faruwa a Rivers. Wani da ba a zaɓa ba zai sauke wanda aka zaɓa. Ka duba abin da ke faruwa a majalisar dattawa. Sanatan da aka zaɓa zai sauke sanatar da aka zaɓa."
"Ina cewa, laifin wanene yanzu? Laifinmu ne. Ƴan Najeriya sun bar su suna yin yadda suka ga dama, kuma idan kana magana suka kama ka, za su tsare ka a ɓoye, kamar yadda na taɓa ɗanɗanawa."
"Shin talauci ko yunwa yana bambanta Bayarabe Igbo ko Bahaushe? Duka muna ciki. Saboda haka, dole ne mu cire wasu son zuciya mu yi aiki don ceto tsarin, ba wai don mutum guda ba."
- Buba Galadima
Buba Galadima ya musanta komawar Kwankwaso APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar APC ya yi magana kan rahotannin da ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC.
Buba Galadima ya musanta rahotannin waɗanda ke cewa tsohon gwamnan na juhar Kano zai koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
Babban ƙusan na NNPP ya ƙara da cewa babu wani mutum wanda ya san abin da yake yi da zai yi alfahari da APC a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Umar Ganduje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng