2027: Buba Galadima Ya Magantu kan Yiwuwar Haɗakar Kwankwaso da Ƴan Adawa
- Injiniya Buba Galadima ya ce ba za su amince su dauko wani azzalumi ba domin mulkin Najeriya, ko da suna adawa da gwamnati
- Galadima ya nuna cewa haɗakar jam’iyyu za ta iya yiwuwa, amma fa sai dai idan waɗanda za a haɗa da su suna da ra’ayi irin nasu
- Jigon NNPP mai alamar littafi ya ce Kwankwaso mutum ne mai kishin Arewa da Najeriya, kuma ko makiyansa sun yarda da hakan
- Ya jaddada cewa su ba su sauri a neman mulki, ya ba da misali da yadda Muhammadu Buhari ya dade kafin ya samu mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jigon jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya yi magana kan shirin hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya.
Buba Galadima ya ce ko kadan ba za su amince da barin azzalumi kuma su sake dauko wani ya shugabanci Najeriya ba.

Asali: Facebook
Buba Galadima ya fadi tasirin Kwankwaso a siyasa
Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin hira da ya yi da DCL Hausa da aka wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Galadima ya ce za su iya haɗaka amma da masu akida irin tasu kuma masu tausayin talakawa da ba za su bari a wawure dukiyar al'umma ba.
Jigon NNPP ya ce har makiyan Rabiu Kwankwaso sun sani yana da kishin Arewa da kuma Najeriya baki daya.
Ya bukaci manyan kasar su zo su mara masa bayan duba da yadda yake samun yabo ta kowane ɓangare.
A cikin hirar, Buba Galadima ya ce:
"APC ba jam'iyya ba ce? Mu ba jam'iyya ba ce? mutane suna ta cewa Kwankwaso mutumin kirki ne yana da kishin Arewa da Najeriya har makiyansa sun sani, amma jam'iyyarsa karama ce, to su shigo su mara masa baya.
"Mu fa ba za mu yi haɗaka da ƴan jari-hujja kawai domin muna kin wani ɗan jari-hujja mu dauko wanda ya fi shi muni, mu daura ba, ba za mu yi haka ba."

Asali: Facebook
Buba Galadima ya bugi kirji kan mulkin Najeriya
Buba Galadima ya ce kowa ya sani da shi da Rabiu Kwankwaso tafiyar ra'ayi da kuma akida suke yi domin talaka ya ji dadi a rayuwarsa.
Kan maganar lashe zabe, duba da fadin Najeriya, Buba Galadima ya ce babu abin Allah ba zai iya yi ba saboda zai iya mayar da talaka ya zama Sarki.
Har ila yau, Buba ya ce su ba sauri suke yi ba saboda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sau nawa ya nemi mulki kafin Allah ya ba shi.
Buba Galadima ya soki faduwar farashin abinci
Kun ji cewa jigo a siyasar Kwankwasiyya, Injiniya Buba Galadima, ya ce saukar farashin abinci da ake gani a halin yanzu na iya haifar da matsaloli a nan gaba.
Injiniyan ya ce shigo da kayan abinci daga kasashen waje zai kassara manoma Najeriya tare da durkusar da masana’antun sarrafa abinci a kasar baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng