Bayan Ganduje Ya Tabo Batun Zuwan Kwankwaso APC, Ɗan Majalisa Ya Dawo Jam'iyyar
- Jam’iyyar PDP ta sake fuskantar koma baya a Edo bayan dan majalisar dokoki, Nicholas Asonsere ya sauya sheka zuwa APC
- Asonsere ya ce ayyukan alheri da Gwamna Monday Okpebholo ke yi ya karfafa masa gwiwar barin PDP don marawa ci gaban yankinsa baya
- Mukaddashin shugaban APC a Edo, Jarrett Tenebe, ya bayyana sauya shekar a matsayin girgiza ga PDP, yana yabawa Asonsere kan jajircewarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Jam’iyyar PDP ta sake fuskantar koma baya a jihar Edo bayan rasa dan majalisar dattawa zuwa APC.
Dan majalisar mai wakiltar Ikpoba-Okha, Nicholas Asonsere, ya yi watsi da lamarin PDP mai adawa inda ya koma jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
'Dan majalisa daga Edo ya koma APC
Asonsere ya samu tarba a hukumance a sakatariyar APC ta jihar da ke Benin daga mukaddashin shugaban jam’iyyar, Jarrett Tenebe da sauran shugabanni, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da wannan sauya sheka, APC na da kujeru 15 a majalisar dokokin Edo, yayin da PDP ta ragu zuwa kujeru tara.
Asonsere ya bayyana cewa ci gaban da Gwamna Monday Okpebholo ke kawowa musamman gadar Ramat Park ne ya kara masa karfi ya koma APC.
Ya ce:
“Na shiga APC ne da gamsuwa ta kaina, wannan ne na fada wa gwamna jiya da dare lokacin da na kira shi da kaina.
“Ba zan tsaya gefe ba yayin da wani ke cigaban yankina kai tsaye. Dole ne in goyi bayan wanda ke wakiltar bukatun jama’ata.”

Asali: Twitter
Musabbabin sauya shekar dan majalisa zuwa APC
'Dan majalisar ya ce burinsa ne ya ja hankalin al’umma domin su marawa gwamna baya wajen kammala ayyukan da ya fara a yankinsa.
Ya ce sauya shekar tasa na da nufin kawo hadin kai da ci gaba a tsakanin ‘yan majalisar jihar.
Ya kara da cewa:
“Ga abokan aikina a majalisa, bana so su fara kallona a matsayin wanda ke hana ci gaba. Mu hada kai mu tallafa wa jihar.”
A nasa bangaren, mukaddashin shugaban APC, Jarrett Tenebe ya bayyana sauya shekar Asonsere a matsayin wani sabon babban abu a tarihin siyasar jihar Edo.
Ya ce:
“Sabon girgiza ya sake afkawa PDP. Tare da ficewar Nicholas Asonsere, PDP ta rasa daya daga cikin muryoyinta mafi tasiri.”
Tenebe ya yaba da matakin Asonsere na hada kai da Gwamna Okpebholo don gina Edo mai alfahari da ita a kowane mataki.
Ya tabbatarwa da al’ummar jihar Edo cewa sun shiga sabon zamani mai kyau karkashin jagorancin Gwamna Okpebholo.
Sanata Sumaila ya magantu kan komawa APC
Kun ji cewa Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana matsayarsa kan kiran da shugabannin APC suka yi masa.
Sanata Sumaila ya bayyana cewa ya fara neman shawarwari daga mutanen mazaɓarsa domin yanke shawara game da komawa jam'iyyar APC.
Sumaila da ke jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa duk abin da mutanen mazaɓarsa suka yanke, to da shi zai yi amfani a matsayin makomarsa a siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng