Mene Ake Kitsawa?: Barau Ya Gana da Baffa Bichi da Tsohon Kwamishinan Abba

Mene Ake Kitsawa?: Barau Ya Gana da Baffa Bichi da Tsohon Kwamishinan Abba

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, da Muhammad Diggol sun kai ziyara ga Sanata Barau Jibrin a gidansa da ke Abuja
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen cimma cigaba mai ɗorewa a Kano da Najeriya
  • Taron bangarorin ya kasance wani bangare na kokarin hada kan manyan jiga-jigan siyasa don inganta ci gaban jihar Kano
  • Ziyarar ta jawo martani daga wasu, kasancewar an haɗa manyan 'yan APC da jiga-jigan jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi bakuncin tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano.

Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da tsohon Kwamishinan Bibiya da Tantance Ayyuka, Muhammad Diggol, sun ziyarci Barau ne a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Barau ya karbi bakuncin tsohon sakataren gwamnatin Kano
Sanata Barau Jibrin ya gana da Dakta Baffah Bichi a Abuja. Hoto: Barau I Jibrin.
Asali: Facebook

Mawakan Kwankwasiyya sun koma APC a Abuja

Sanata Barau Jibrin shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 14 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan mawakan Kannywood, Adamu Hassan Nagudu da Yusuf Karkasara sun sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Mawakan sun bayyana ficewarsu daga Kwankwasiyya yayin wata ziyarar da suka kai wa Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja.

An ce bayan sauya shekar, sun kafa kungiyoyi biyu masu suna 'Naka Sai Naka' da 'Barau Mafita' domin tallata ayyukan jam’iyyar APC.

Barau ya bukaci hadin kai domin ci gaba

Tsofaffin jiga-jigan gwamnatin na Kano sun gana da Sanata Barau I. Jibrin ne wanda kuma jigo ne a jam'iyyar APC.

Barau ya jaddada bukatar haɗin gwiwa domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

A cewar Sanata Barau:

“Ci gaban jiharmu da ƙasa na kasancewa a sahun gaba a tsare-tsaremu, za mu ci gaba da haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki."
Barau Jibrin ya yi muhimmiyar ganawa da Dakta Baffa Bichi
Sanata Barau Jibrin ya hana tsofaffin jiga-jigai a gwamnatin jihar Kano. Hoto: Barau I Jibrin.
Asali: Facebook

Kano: An yi hasashen hadin guiwar yan siyasa

Rahotanni sun bayyana cewa wannan ganawa na daga cikin yunkurin jiga-jigan siyasa na ganin an samu fahimta da haɗin kai a Kano.

Taron ya kuma ja hankalin jama’a, ganin yadda wasu manyan ‘yan APC suka hadu da jiga-jigan jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano.

An bayyana wannan ganawa a matsayin wani mataki na ganin an cimma ci gaba da tsare-tsaren da za su amfani jihar da kasa baki ɗaya.

Hotuna daga ganawar sun nuna jituwa da girmamawa a tsakanin sassan biyu, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama'a daban-daban.

Barau ya karbi malaman Kwankwasiyya zuwa APC

Kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya karɓi wasu jiga-jigan kungiyar malaman Kwankwasiyya guda 23 zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

'Yan uwan Gwamnan Kano, ciki har da Mahbub Nuhu Wali, sun bar NNPP inda suka shiga APC tare da jefar da jajayen huluna.

Bayan ganawa a Majalisa, sun raka shi 'A-Class Event Centre' inda shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya tarbi magoya bayan Atiku Abubakar daga jihohi 19 na Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng