An Fara Cike Fom domin Samun Tallafin Noman Naira Miliyan 1 na Sanata Barau
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da shirin tallafawa matasa da rancen noma a Arewa maso Yamma
- Rahotanni sun nuna cewa za a zabi matasa 558 daga kananan hukumomi 186 a jihohin yankin da ya fito don ba su rance daga N1m zuwa N5m
- Bayanai sun tabbatar da cewa shirin yana da nufin inganta noma da samar da abinci, tare da hadin gwiwar Bankin Noma na Najeriya (BOA)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata Barau Jibrin ya sanar da bude tsarin bada rance ga matasa domin bunkasa noma a Arewa maso Yamma.
Shirin tallafin Barau mai suna BIARN na da nufin taimakawa manoma matasa su habaka harkar noma a Arewacin kasar nan.

Asali: Twitter
Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske kan yadda za a cike fom din shirin a wani sako da ya walllafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A karkashin shirin, za a tantance matasa uku daga kowace karamar hukuma cikin 186 a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara.
Wadanda suka cancanta za su samu rance daga N1m zuwa N5m domin amfani da shi a gonakinsu.
Alakar shirin noman da gwamnatin Tinubu
Sanata Barau ya bayyana cewa shirin yana tafiya ne tsarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci da aikin yi.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce sun rattaba yarjejeniya da Bankin Noma na Najeriya (BOA) domin tabbatar da shirin.
Kyauta Barau zai ba da kudin tallafin?
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa shirin BIARN zai bai wa matasa damar samun rance mai tsoka domin bunkasa harkar noma a Arewa maso Yamma.
Ya ce kowace karamar hukuma daga cikin 186 da ke yankin za ta samu matasa uku da za a tallafa wa, wanda hakan ke nufin mutum 558 za su ci gajiyar shirin a bana.
Za a yi la'akari da yanayin gona
Sanata Barau ya ce wadanda suka cancanta za su samu rance daga N1 miliyan zuwa N5 miliyan bisa la’akari da irin gonakin da suke da su da kuma bukatunsu.
Ya ce burin shirin shi ne bunkasa noma, samar da wadataccen abinci da kuma rage matsalar rashin aikin yi da ke addabar matasa a yankin Arewa maso Yamma.

Asali: Facebook
Yadda za a cike fom din shirin noman
Sanata Barau ya bayyana cewa shirin yana gudana ne tare da hadin gwiwar Bankin Noma na Najeriya (BOA), kuma an riga an rattaba yarjejeniya domin aiwatar da shi.
A karkashin haka aka bukaci matasan da ke sha’awar shiga shirin su garzaya su cike fom a nan domin samun dama.
Tinubu zai dauki matasa aiki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi alkawarin daukan aiki ga matasa 774 da aka zakulo daga dukkan kananan hukumomi domin aikin wucin gadi.
Za a ba matasan aikin gwamnati ne idan suka kammala aikin sa-ido a kan cibiyoyin lafiya da ke fadin Najeriya da ma'aikatar lafiya ta dauke su domin su gudanar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng