Barau Ya Karbi Sakataren Malaman Kwankwasiyya da 'Yan Uwan Abba a APC
- Sanata Barau Jibrin ya karɓi wasu jiga-jigan kungiyar malaman Kwankwasiyya guda 23 zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- ‘Yan uwan Gwamnan Kano, ciki har da Mahbub Nuhu Wali, sun bar NNPP inda suka shiga APC tare da jefar da jajayen huluna
- Bayan ganawa a Majalisa, sun raka shi 'A-Class Event Centre', suka tarbi magoya bayan Atiku Abubakardaga jihohi 19 na Arewa
- Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya karɓi shugabannin NNPP daga Gwale, yayin da Barau ya jaddada aniyarsa ta kawo ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya sake yi wa jam'iyyar NNPP da Kwankwasiyya illa.
Sanata Barau Jibrin ya karbi Sakataren 'Kwankwasiyya Ulama Forum', Malam Yahaya Abdulkadir Aliyu, tare da shugabannin kungiyar guda 23 zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Ana raɗe radin Atiku ya bar PDP, Ganduje da Barau sun sharewa Tinubu hanya a jihohi Arewa 19

Asali: Facebook
Ganduje ya karbi 'yan PDP zuwa APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar 8 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan karbar 'wasu yan a mutun Atiku Abubakar daga jihohin Arewa 19 da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi.
Gamayyar kungiyoyin magoya bayan Atiku Abubakar a jihohin Arewa 19 sun fice daga jam'iyyar PDP, sun koma APC mai mulkin Najeriya.
Dr. Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin ne suka tarbi masu sauya shekar a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Yadda 'yan Kwankwasiyya suka koma jam'iyyar APC
Haka nan, Barau ya karɓi wasu ‘yan uwan Gwamnan Jihar Kano ciki har da Mahbub Nuhu Wali, inda suka sauya sheka zuwa APC.
Dukansu sun jefar da jajayen hulunan Kwankwasiyya yayin ziyarar da suka kai masa a Majalisar Tarayya ranar Juma’a da ta gabata.
Bayan taron, Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓe su a hukumance a matsayin sabbin ‘yan jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Barau ya yi alkawari ga sabbabbin shiga APC
Haka nan, manyan jiga-jigan NNPP daga Gwale, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale, sun koma APC tare da amincewar Ganduje.
A cikin sanarwar, Barau ya ce:
"A matsayina na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, na jaddada kudirina na kawo ci gaba ga mutanen Kano ta Arewa, jihar Kano, da kasa baki ɗaya.
"Ina mai jaddada cewa ni Sanata ne ga kowa, ba tare da la’akari da jam’iyya ba. Idan kuna son shigowa APC, muna maraba da ku."
Ganduje ya sha alwashin jana'izar PDP
Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa PDP mai adawa a Najeriya na dab da rugujewa.
Shugaban jam'iyyar ya ce PDP ta mutu murus saboda rikicin cikin gida da ya addabe ta, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Ganduje ya nuna hakan da cewa ya fito fili a jihar Anambra inda jam'iyyar ta kasa samun ɗan takara a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng