Yunkurin Tsige Gwamna Ya Jefa Shugaba Tinubu a Matsala, An Yi Masa Barazana
- Ƴan kalibar Ijaw sun yi barazanar ɗaukar matakin da zai ba Shugaban Kasa, Bola Tinubu mamaki idan ya sake aka tsige Gwamna SImi Fubara
- Wata kungiyar ƴan Ijaw, mai rajin kare al'adu ta bayyana cewa da sanin Tinubu ne Wike ya ke abin da ya ga dama a rikicin siyasar jihar Ribas
- A cewar ƴan kabilar, kotu ƴar amshin shatar Wike ce shiyasa aka yanke hukunci daidai da yadda yake so da Mai girma Fubara ya yi kara a kotu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Kalaman Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike cewa ba abin da zai faru idan aka tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas sun tayar da ƙura.
Supreme Egbesu Assembly (SEA), wata ƙungiyar ƴan kabilar Ijaw, ta yi barazanar cewa za ta "ba Shugaba Bola Tinubu mamaki a lokacin da ya dace" idan aka tsige gwamnan.

Asali: Facebook
Abubuwan da ke faruwa a Ribas
Wannan dai na zuwa ne bayan rikicin siyasar jihar Ribas ya kara dawowa ɗanye tun bayan hukuncin kotun kolin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma a ranar Laraba da ta gabata, ƴan Majalisar Dokoki 27 na tsagin Wike, waɗanda kotun koli ta tabbatar da sahihancinsu, suka hana Fubara shiga zauren Majalisa.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da Gwamna Fubara ya isa Majalisar da nufin sake gabatar da kasafin kudin 2025 kamar yadda kotun ƙoli ta umarta.
Kwatsam sai aka ji ministan Abuja, Wike na cewa idan Fubara ya aikata laifin da ya cancanta a tsige shi, babu abin da zai faru don ƴan Majalisa sun tunbuke shi.
Kungiyar SEA ta caccaki Wike da Tinubu
Shugaban SEA, Werinipre Digifa, ya yi Allah-wadai da kalaman Wike, yana mai zargin cewa yana nuna girman kai da rashin hankali a kan al’ummar Ijaw.
A cewarsa:
"Tinubu ne ke da alhakin wannan girman kai da rashin da’a da Wike ke nunawa a kan mutanen kabilar Ijaw.
"Wike ya riga ya san yadda hukuncin kotun koli zai kasance kafin a yanke shi, kuma haka ya faru daidai da yadda yake so. Wannan ya tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce da ba ta da tsarin doka da oda."

Asali: Facebook
Mutanen Ijawa sun yi wa Tinubu barazana
Digifa ya ce mutanen Ijaw ba su da dabi'ar tada rikici, amma za su fuskanci lamarin cikin lalama da kuma dabaru masu kyau.
"Muna lura da irin cin mutuncin da ake wa gwamnan jihar Rivers da kuma kalaman batanci da ake yi wa mutanen ƙabilar Ijaw. Mutanen Neja Delta suna da fahimta.
"Kuma idan matsala ta taso, manya ba su gaggauta shiga. A al’adar Afirka, ana cewa ‘mahaukata biyu ba lokaci guda suka haukace ba'. Don haka mu muna lura da abubuwan da ke faruwa."
Duk da haka, kungiyar ta bayyana cewa ba za ta dauki matakin tashin hankali ba, amma za ta dauki matakan da suka dace a siyasance domin kare mutuncin mutanen Ijaw.
Shugaba Tinubu ya bukaci a bi umarnin doka
A baya kun ji cewa, Bola Tinubu ya buƙaci shugabannin yankin Kudu maso Kudu su tabbatar da an bi hukuncin kotun ƙoli domin warware rikicin jihar Ribas.
Shugaban ƙasar ya ba da wannan shawara ne yayin wata ganawa da shugabannin yankin Neja Delta karkashin kungiyar PANDEF a Aso Rock da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng