Sanata Ya Watsawa Matasa Kasa a Ido, Ya Ki Amincewa Ya Kara da Tinubu a 2027
- Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa ba shi da sha’awar yin takarar shugaban Najeriya a 2027 biyo bayan kiraye kirayen wasu matasan kasar nan
- Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar raya yankin Kudu maso Gabas ya fadi haka ne a matsayin martani ga bukatar kungiyar NYLF
- Kungiyar ta roki Sanatan ya fito takara, tare da daukar gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ko na Adamawa, Ahmadu Fintiri a matsayin mataimakinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar raya yankin Kudu maso Gabas, Orji Uzor Kalu, ya yi watsi da kiran da ƙungiyar NYLF ta yi masa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.
NYLF, wacce ta hada kungiyoyi akalla 40, ta bukaci tsohon gwamnan jihar Abia da ya yi la’akari da yin takara tare da gwamna Dauda Lawal na Zamfara ko Ahmadu Fintiri na Adamawa a matsayin mataimakinsa.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa, wannan ƙungiya ta yi wannan roko ne a ranar Laraba, bayan wata ziyarar ban girma da suka kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, Jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun nemi Sanata Kalu ya fito takara
Jaridar Vanguard ta ruwaito shugaban NYLF, Kwamared Eliot Afiyo, ya bayyana Kalu da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, a matsayin waɗanda suka fi dacewa da shugabancin Najeriya a 2027.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran Kalu ya fitar a ranar Alhamis, Sanatan ya yi watsi da wannan kira, yana mai cewa bai da sha’awar shiga takarar shugabancin ƙasa.
Dalilin Sanata na watsi da kiran matasa
Sanarwar da ofishin Sanata Kalu ya fitar ta jaddada cewa yana goyon bayan manufofin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, musamman a fannin tattalin arziƙi.

Asali: Facebook
Sanarwar ta ce:
"Sanata Kalu ya bayyana matsayarsa a fili game da zaɓen 2027 kuma yana gargadin ‘yan adawa da su guji kawo cikas ga ci gaban ƙasa."
Har ila yau, Kalu ya nanata cewa shugaban ƙasa na buƙatar wa’adi biyu domin tabbatar da ingantaccen ci gaba, musamman a fannin tattalin arziƙi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Kalu na da yakinin cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Shugaba Tinubu zai haifar da da mai ido. Ya fahimci cewa dorewar waɗannan sauye-sauyen na buƙatar zaman lafiyar siyasa da haɗin kai.
Shugaban ƙasa na buƙatar cikakken wa’adin shekara takwas domin cimma wadannan manufofi."
Wannan na nuni da cewa, duk da matsin lamba daga wasu ƙungiyoyin matasa, Sanata Kalu ya fi mayar da hankali kan goyon bayan gwamnati mai ci fiye da shiga takarar 2027.
Sanata ya dira kan matasa kan Natasha
A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya soki ‘yan Najeriya da ke yin sharhi kan dambarwar dakatar da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan.
Ya kwatanta muhawarar da ake yi da irin tattaunawar magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, ya ce da dama daga cikin masu magana ba su da cikakken sani kan harkokin majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng