Bayan 'Wulakacin' da Aka Masa, Gwamna Ya Aika Wasiƙa ga Majalisar Dokoki
- Gwamna Siminalayi Fubara ya sake tura wasiƙa a hukumance ga Majalisar Dokokin jihar Ribas kan batun gabatar da kasafin 2025
- A wasiƙar mai ɗauke da kwanan 13 ga Maris, 2025, Fubara ya ce zai sake zuwa Majalisar ranar Laraba ta makon gobe domin cika umarnin kotu
- Wannan dai na zuwa ne bayan an hana Gwamna Fubara da mutanensa shiga wurin da Majalisar ke zama ranar Laraba da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamnan Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya sake aika wasiƙa zuwa ga Majalisar Dokokin jihar ranar 13 ga watan Maris, 2025.
Gwamna Simi Fubara ya sanar da ƴan Majalisar cewa zai sake dawowa ya gabatar da kasafin kudin 2025 domin tantancewa da amincewa.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta ce gwamnan ya aika wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Maris, 2025 zuwa ga kakakin Majalisar dokoki, Hon. Martins Amaewhule.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe Gwaman Fubara zai koma Majalisa?
Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya shirya dawowa ya gabatar da kasafin kuɗin a ranar Laraba, 19 ga Maris, 2025, ko kuma a wata rana daban da majalisar ta zaɓa a cikin watan Maris.
Gwamnan ya ce sake gabatar da kasafin kuɗin ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli da kuma bukatar 'yan majalisar da suka nemi ya sake gabatarwa.
Fubara ya kuma tuna yadda ya yi ƙoƙarin gabatar da kasafin kuɗi a baya amma aka hana shi shiga zauren Majalisar Majalisar Dokoki na wucin gadi da ke Fatakwal.
An hana gwamna shiga Majalisar Rivers
A ranar Laraba da ta gabata, Gwamna Fubara ya gamu da tangarɗa yayin da ya isa Majalisar Dokokin jihar Ribas da ke Fatakwal, rahoton Channels tv.
An tattaro cewa jami’an tsaro sun kulle ƙofar shiga, lamarin da ya hana Gwamna Fubara da tawagarsa samun damar gabatar da kasafin kuɗin 2025.
Rahotanni sun nuna cewa Fubara ya je majalisar ne domin sake gabatar da kasafin kuɗi, kamar yadda hukuncin Kotun Koli na 28 ga Fabrairu, 2025, ya tanada.
Sai dai bisa mamaki aka hana shi shiga, wanda a cewar Jami'an tsaron da ke gadin Majalisar an rufe ƙofa ne saboda gwamnan bai sanar da zuwansa ba.
Fubara ya aika wasiƙa ga Majalisar dokoki
Wannan lamari dai ya tayar da kura a siyasar jihar Ribas amma Gwamna Fubara ya ce duk da haka zai sake komawa domin cika umarnin kotun ƙoli.
Hakan ya sa ya sake tura wasiƙa zuwa ga Shugaban Majalisar, yana neman izinin sake dawowa domin gabatar da wannan kasafin kudi.
Yanzu dai ana jira a ga ko majalisar za ta amince da sabon lokacin da gwamnan ya bada domin gabatar da kasafin kuɗin na 2025 ko kuma za ta canza lokaci.
Gwamna Fubara ya maidawa Majalisa martani
A baya, kun ji cewa Gwamna Simi Fubara ya tunawa ƴan Majalisar Dokokin jihar Ribas cewa komai mai ƙarewa ne, akwai ranar da shi da su za su bar mulki.
Gwamnan ya jaddada cewa ya bi duk matakan da suka dace domin warware matsalar, yana mai bayyana fatan cewa ‘yan majalisar za su mutunta hukuncin kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng