APC Ta Kwato Sakatariyarta da PDP ta Mamaye da Karfi na Tsawon Shekaru

APC Ta Kwato Sakatariyarta da PDP ta Mamaye da Karfi na Tsawon Shekaru

  • Jam’iyyar APC ta karbe ofishinta da ke hanyar filin jirgin saman Birnin Benin daga hannun PDP bayan shekaru huɗu
  • Shugabannin APC sun bayyana cewa sun bi doka wajen sabunta hayar ginin na tsawon shekaru bakwai kafin PDP ta mamaye shi
  • Shugaban APC na jihar Edo ya yi alkawarin kare dukiyar jam’iyyar daga duk wata barazana daga 'yan adawa da sauran mutane

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta samu nasarar karbe ofishinta da ke Birnin Benin daga hannun jam’iyyar PDP.

Ginin da aka fi sani da hedikwatar APC, ya fada hannun PDP ne bayan gwamna Godwin Obaseki ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a shekarar 2020.

Ganduje
APC ta kwato ofishin da PDP ta kwace mata. Hoto: Salihu Tanko Yakasai|Official PDP
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban APC na jihar Edo ya tabbatar da kwato ofishin yana mai cewa ginin ya kasance mallakarsu tsawon shekaru kafin PDP ta mamaye shi da karfi.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin shugaban APC na jihar Edo

A lokacin da yake jawabi bayan kwato ginin, shugaban APC na jihar, Jarrett Tenebe ya ce sun riga sun sabunta kudin hayar sakateriyar.

Jarrett Tenebe ya ce;

“Tun shekaru huɗu da suka wuce, APC ta yi kokari wajen sabunta hayar wannan gini, wanda ko yaushe yake zama ofishin jam’iyyar.
Idan ku ka bincika a Google, za ku ga cewa har yanzu wannan wuri yana a matsayin hedikwatar APC.”

The Guardian ta rahoto cewa shugaban ya ce ofishin jam’iyyar APC na kasa ya bayar da tallafin kudi domin sabunta hayar ginin, wanda hakan ya tabbatar da cewa ginin na APC ne.

Sai dai Tenebe ya yi zargin cewa bayan Gwamna Obaseki ya koma PDP, jam’iyyar hamayyar ta yi amfani da karfi wajen mamaye ginin.

“A lokacin, sun lalata kayan APC, sun kwace motocin jam’iyyar, sannan suka kori mambobinmu daga ginin.”

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

- Jarrett Tenebe

APC ta zargi tsohon gwamnan jihar Edo

Jarrett Tenebe ya bayyana cewa sun rubuta korafi zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, wanda ya bayar da umarnin cewa a mayar wa APC da ofishinta.

Duk da haka, ya ce tsohon kwamishinan ‘yan sanda na jihar, karkashin ikon gwamna Obaseki, ya hana su amfani da ginin.

“Wannan abu ya kasance daga cikin abubuwan da muka fi mayar da hankali a kansu bayan na zama shugaban APC a jihar Edo,”

- Jarrett Tenebe

Shugaban ya kuma yi alkawarin kare dukiyar APC daga duk wata barazana daga kowace kungiya ko mutum.

Me jam'iyyar PDP ta ce kan lamarin?

Bayan karbar ofishin, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta yi karin bayani game da lamarin idan lokaci ya yi.

Kakakin rikon kwarya na PDP, Chris Nehikhare ya ce za su fitar da sanarwa, amma har lokacin kammala wannan rahoto ba su fitar da komai ba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Ɗan takarar gwamnan PDP ya maka shugaban APC a kotu, yana neman N500m

Shirin APC na kare dukkannin dukiyar jam’iyyar

A karshe, Jarrett Tenebe ya jaddada kudirin APC na kare dukkannin kadarorin jam’iyyar a jihar Edo, yana mai cewa,

“Za mu tabbatar da cewa dukkan barnar da PDP ta yi karkashin Gwamna Obaseki an gyara ta.”

Karbar wannan gini ya nuna sabon karfi ga APC a jihar Edo yayin da jam’iyyar ta karbe madafun iko a zaben gwamnan jihar da ya gabata.

APC da PDP sun zargi juna a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyun PDP da APC sun zargi juna da tayar da fitina yayin da aka fara sauraron karar gwamnan jihar Edo.

An ruwaito cewa zargin ya biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai ne yayin da ake zaman kotun sauraron shari'ar da aka shigar da APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng