Sojojin Kamaru Sun Yi Kuste Najeriya, Dakarun Kasar Sun Dauki Mataki

Sojojin Kamaru Sun Yi Kuste Najeriya, Dakarun Kasar Sun Dauki Mataki

  • Tashin hankali ya mamaye al’ummar Danare da ke karamar hukumar Boki ta jihar Cross River a ranar Laraba bayan ganin wasu sojojin Kamaru
  • Rahoto ya nuna cewa an ga sojojin dauke da makamai sun shiga garin da ke kan iyaka tare da harba bindigogi a sama yayin wata takaddama
  • Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da lamarin, inda ta bukaci kowa ya kwantar da hankalin shi domin an riga an shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta ce ta shawo kan rikicin da ya biyo bayan kutsen da wasu sojojin Kamaru suka yi ba tare da izini ba cikin al’ummar Danare da ke karamar hukumar Boki ta jihar Cross River.

Rundunar ta ce lamarin, wanda ya faru ranar Talata, an gaggauta dakile shi ta hannun sojojin Najeriya da ke aikin sintiri a yankin, lamarin da ya hana rikicin kara kamari.

Kara karanta wannan

Iran ta rufe Hormuz gaba daya, ta farmaki jiragen da suka yi taurin kai

Hafsun tsaron Najeriya tare da sojoji
Laftanar Janar O. Oluyede tare da dakarun Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 82 , Laftanar Kanar Olabisi Ayeni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Enugu ranar Alhamis.

Bayani kan kutsen sojin Kamaru

A cewar Ayeni, sojojin da ke Danare sun dauki mataki bayan samun rahoton kasancewar sojojin Kamaru a cikin al’ummar, inda suka tuntubi hukumomin soja da suka dace a Kamaru nan take.

Ya ce wannan tuntuba ta kai ga janye sojojin kasashen waje daga yankin Najeriya bisa ka’idojin da aka tanada kan iyakoki.

Ayeni ya ce binciken farko ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga sabani kan karbar haraji daga gonaki da ke tsakanin al’ummar Danare a Najeriya da al’ummar Dadi a Kamaru.

The Sun ta rahoto ya ce rundunar ta bayyana cewa tattaunawar ta taimaka wajen karfafa hadin kai a kan iyaka, fayyace hanyoyin gudanar da ayyuka a kan iyakar da kuma hana sake faruwar irin wannan lamari.

Kara karanta wannan

"Sun samu shahada": Jirgin sama dauke da mutane ya gamu da hatsari a Pakistan

Sojojin kasar Kamaru a bakin aiki
Dakarun Kamaru a kauyen Mabass da ke Arewacin kasar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sojoji za su kare Najeriya

Ayeni ya sake jaddada kudirin runduna ta 82 na kare cikakken ikon Najeriya a yankunanta da kuma tabbatar da tsaron al’ummomin da ke karkashin yankin aikinta.

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa zaman lafiya ya dawo a Danare da makwabtan ta, yana mai cewa sojoji na ci gaba da sanya ido da kuma bibiyar duk wasu abubuwan da ke faruwa a kan iyakar.

Sojoji sun bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu na halal, tare da gujewa yada bayanan da ba a tabbatar da su ba wadanda ka iya jefa jama’a cikin fargaba.

Atiku ya yabawa Sojojin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yabawa rundunar sojin Najeriya bayan ceto mutane 360 a jihar Borno.

Rundunar sojin ta tabbatar da ceto mutanen daga tsaunukan Mandara, wani sansanin ‘yan ta’adda da ya yi kaurin suna a Kudancin jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce ya yi matukar farin ciki da rahoton ceto mutane 360 din, inda ya yabawa sojoji kan farmakin da suka kai wa ‘yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng