'Ku Tsige Shi': Minista Ya Bukaci Majalisa Su Tuge Yaronsa daga Kujerar Gwamna

'Ku Tsige Shi': Minista Ya Bukaci Majalisa Su Tuge Yaronsa daga Kujerar Gwamna

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce idan Simi Fubara ya aikata laifi, majalisa ta tsige shi, domin ba laifi ba ne a siyasa
  • Wike ya nuna damuwa da yadda wasu 'yan majalisa uku ke ƙoƙarin kafa doka, yana mai sukar matakin zuwa kotun koli
  • Ya ce Gwamna Fubara ya raina dattawan da suka taimaka masa, kuma ya na zargin abokan aikinsa da cin moriyar jihar
  • Wike ya kalubalanci PANDEF, yana mai cewa ƙungiyar na hana kokarin sasancin Bola Tinubu da kuma ɓata siyasar yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi magana kan rigimar siyasa da dambarwa da ke faruwa a jihar Rivers.

Nyesom Wike ya ce ya kamata a tsige Gwamna Siminalayi Fubara idan ya aikata abin da ya cancanta a raba shi da kujerar.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan Jigawa ya kai ziyara wajen raba abinci, ya gano abin mamaki

Wike ya caccaki Fubara kan rigimar Rivers
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya nuna damuwa kan rigimar siyasa a Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike.
Asali: Facebook

Wike ya zargi Fubara da cin amana

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da manema labarai, ya nuna damuwarsa kan rikicin siyasa da ke faruwa a jihar Rivers, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya koka kan yadda rikicin ya ki karewa inda yake zargin wasu da ci gaba da ruruta rigimar domin biyan buƙatar kansu.

Wike ya tuna yadda dattijo Ferdinand Alabararba ya yi ƙoƙarin ganin dan Ijaw ya zama gwamna, amma daga baya aka ci mutuncinsa.

Ya kare kansa cewa yana mutunta doka da oda, yana mamakin yadda 'yan majalisa kaɗan ke ƙirƙirar doka da kuma neman hukuncin kotu.

Wike ya ce:

“Wannan dattijo har da kuka, wannan yaron daga baya ya zazzage shi, yanzu ba zai iya komawa ya nemi taimakonsa ba.
“Ina mamakin yadda a kasar nan, mutane uku za su kafa doka, su kuma je kotun koli."
Wike ya caccaki dattawan Kudu maso Kudu da ruruta rigimar Rivers
Nyesom Wike ya bukaci majalisa ta tsige Gwamna Siminalayi Fubara idan ya yi laifi. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike.
Asali: Facebook

Wike ya fadi yadda ake tafiyar da siyasa

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana bayan APC ta yi barazanar tsige gwamnan PDP

Wike ya yaba wa masu kalubalantar abin da bai dace ba, yana mai jaddada cewa ‘yan majalisa ba bayi ba ne, an zaɓe su ne kamar kowa, cewar Channels TV.

Wike ya kara da cewa:

“Shugabannin majalisa ba yaranmu ba ne, an zaɓe su, na yi tafiya da su, na gina alaƙa da su, ba a matsayin maigida da yaransa ba ne.
"Siyasa ba wasa ba ce. Idan ya aikata abin da ya dace a tsige shi, su tsige shi, tsigewa ba laifi ba ne,”

Wike ya zargi abokan gwamna Fubara da amfani da shi da kuma cin moriyar jihar, yana sukar kungiyar PANDEF da kiranta ƙungiya mafi muni.

Wike ya tada ƙura da cewa ba kowane Ijaw ne ke da rinjaye ba a yankin Neja Delta, yanabayyana bambancin kabilar Kalabari da Opobo.

An hana gwamna Fubara shiga majalisa

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Fubara tare da tawagarsa sun isa Majalisar jihar Rivers a yau Laraba, 12 ga watan Maris, 2025 amma bisa mamaki suka tarar da ƙofofin a rufe.

Kara karanta wannan

SDP: An zargi gwamnan APC da neman marin shugaban jam'iyyar El Rufa'i

Jami'an tsaron da ke gadin Majalisar sun bayyana cewa sun hana gwamnan shiga ne saboda bai turo sanarwar zuwansa a hukumance ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng