Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Sauya Sheƙar El Rufai daga APC zuwa SDP
- Hadimin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na da ƴancin komawa jam'iyyar da yake so
- Da yake martani kan lamarin, Bwala ya ce sauya sheƙar El-Rufai ba wani sabon abu ba ne, yana mai cewa tsohon gwamnan ba zai iya kayar da APC ba
- Wannan martani na Bwala na zuwa ne bayan tsohon sakataren APC na kasa ya raba gari da su, ya ce zai haɗa kai da manyan ƴan adawa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa sauya sheƙar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi daga APC zuwa jam'iyyar SDP ba sabon abu ba ne.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Daniel Bwala ya ce za su binciki dalilin da Nasir El-Rufai ya ambata cewa su suka kore shi daga APC.

Asali: Facebook
Bwala ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter yau Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai na da ƴancin sauya sheƙa
Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa El-Rufai yana da ‘yancin sauya sheka, amma dalilan da suka sa ya fice daga APC su ne za a bincika a cikin kwanaki masu zuwa.
Bwala ya jaddada cewa matakin da El-Rufai ya ɗauka ba wani abu ba ne a siyasar Najeriya, ya na mai cewa ba wani abin mamaki ba ne don ya bar APC kamar walƙiya.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna ya fice daga APC zuwa SDP, ya ce sai da ya shawarci makusantansa kafin ɗaukar wannan mataki.
El-Rufai ya tuna yadda suka kafa jam'iyyar APC kuma suka jagoranci nasarar da ta samu a zaɓukan 2015, 2019, da 2023.
Ya ce a shekaru biyu da suka gabata, APC ta sauka daga manufofin da aka kafa ta a kai kuma duk wani yunkuri na jawo hankalin shugabanni domin a gyara ya ci tura.
Sauya sheƙar El-Rufai ta ja hankalin Bwala
Da yake martanin kan sauya shekar El-Rufai, Daniel Bwala ya ce:
"El-Rufai, na karanta labarin cewa ka fice daga APC zuwa jam'iyyar SDP, ba wani abu ba ne saboda ka na da ƴancin yin abin da ka ga ya fi maka.
"Sai dai za mu gudanar da bincike kan dalilin da suka sa ka bar APC a ƴan kwanaki masu zuwa kuma mu tunatar da ƴan Najeriya cewa ba abin mamaki ba ne dan walkiya ta fito daga sararin sama."

Asali: Twitter
Bwala ya soki shirin El-Rufai na yaƙar APC
Bwala ya kuma caccaki shirin El-Rufai na haɗa kai da ƴan adawa domin kayar da APC a zaɓuka na gaba, yana mai cewa haɗa kai da tulin marasa nasara ba zai kai shi ko
A cewar Bwala, haɗa kai da ‘yan adawa don kifar da gwamnati ba wata sabuwar manufa ba ce ta siyasa, kuma ba alama ce ta ci gaba ba.
Ya ce yunkurin tsohon gwamnan na kifar da APC ba komai ba ne face mafarki da kwaɗayin mulki da ba zai cimma nasara ba.
Tinubu ya roki a sa kasa a addu'a
A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya buƙaci musulmi su ƙara dage wa da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Bola Tinubu ya faɗi haka ne a wurin tafsirin Ramadan da iftar da aka shirya a Ayetoro, hedikwatar ƙaramar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng