Daga Sauya Sheka, El Rufa'i Ya Fadi Yadda zai Jawo Rugujewar APC a Najeriya

Daga Sauya Sheka, El Rufa'i Ya Fadi Yadda zai Jawo Rugujewar APC a Najeriya

  • Malam Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da ficewarsa daga APC tare da komawa jam’iyyar SDP domin ci gaba da fafutuka a siyasa
  • Tsohon gwamnan ya yi alkawarin hada kan jam’iyyun adawa domin fuskantar APC a dukkan zabe daga yanzu har zuwa 2027
  • Masana sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan matakin El-Rufa'i, wasu na ganin ya yi dabara yayin da wasu ke ganin kuskure ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya tabbatar da ficewarsa daga APC tare da komawa jam’iyyar SDP.

A cewarsa, bayan shawarwari da manyan abokan siyasa da magoya bayansa, ya yanke shawarar karbar SDP a matsayin sabon dandalin siyasar sa.

El-Rufa'i
El Rufa'i zai jagoranci adawa da APC a Najeriya. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

El-Rufa’i ya kuma wallafa a shafinsa na Facebook cewa zai yi aiki da sauran jam’iyyun adawa domin hada kai da kalubalantar APC a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Mai jiran gado": Martanin 'yan Najeriya bayan El Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin El-Rufa’i na rusa APC a Najeriya

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Nasir El-Rufa'i ya ce yana fatan hada kan jam’iyyun adawa domin fuskantar APC a dukkan zabuka masu zuwa.

A cewarsa:

“Zan mayar da hankali kan tattaunawa da sauran shugabannin ‘yan adawa domin hada kanmu a dandalin siyasa guda.”

El-Rufa'i ya kuma bukaci magoya bayansa da sauran ‘yan Najeriya da ke neman cigaban kasa su shiga SDP domin taimakawa wajen gina sabuwar siyasa mai inganci.

Ra’ayoyin jama'a a kan ficewar El-Rufa'i

Wani mai sharhi kan siyasa, Abdullahi A. Abdullahi, ya yi nazari kan ficewar El-Rufa'i daga APC zuwa SDP a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki na El-Rufa’i zai ba shi dama ta musamman wajen tsara alkiblar jam’iyyar SDP.

A cewarsa:

“Ba daidai ba ne mutum ya ci gaba da suka kan jam’iyyarsa alhali yana cikinta. Ficewa daga APC ya tabbatar da jajircewarsa kan ra’ayin siyasa.”

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

Sai dai wasu na ganin matakin da El-Rufa’i ya dauka babbar kuskure ne da ka iya kawo karshen tasirin siyasar sa a Najeriya.

Tsohon gwamna
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i. Hoto: Kaduna State Government
Asali: Facebook

Ficewa daga APC: Dabara ko kuskuren El-Rufai?

Wasu na ganin cewa matakin El-Rufa’i dabara ce da zai iya amfani da ita wajen cimma burinsa a siyasa.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin wannan matakin babban kuskure ne a siyasa, domin ficewa daga babbar jam’iyyar da ta ba shi damar mulki na iya raunana tasirinsa a kasa.

A yayin da El-Rufa’i ke kokarin gina wata sabuwar siyasa a SDP, har yanzu ba a san irin goyon bayan da zai samu daga sauran manyan ‘yan adawa ba.

El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya gana da Atiku Abubakar a gidansa.

Rahoton Legit ya nuna cewa Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar ne a lokacin buda baki bayan kammala azumin ranar Lahadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng