Zargin Lalata: Ɗan Majalisar da Ya Jagoranci Dakatar da Sanata Natasha Ya shiga Matsala
- Matasan jam'iyar LP sun bukaci a gaggauta dakatar da shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa, Neda Imasuen
- Shugaban matasan LP na ƙasa, Kennedy Ahanotu ya ce yadda Neda Imasuen ya tafiyar da batun Natasha Akpoti abin kunya ne
- Ya buƙaci al'ummar mazaɓar Edo ta Kudu su gaggauta fara shirin yi wa sanatan kiranye domin ya gaza wakiltarsu yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Shugaban matasa na jam’iyyar LP, Kennedy Ahanotu, ya bukaci a dakatar da Sanata Neda Imasuen mai wakiltar Edo ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Shugaban matasan ya nemi dakatar da sanatan ne bisa abin da ya kira rashin adalci da ya aikata kan batun Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Asali: Facebook
Ahanotu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata a hedkwatar jam’iyyar LP da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Akpabio: Sanatan Arewa ya goyi bayan Natasha kan zargin cin zarafi? An fede gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar LP ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa shafinta na X yau Talata, 11 ga watan Maris, 2025.
Ya ce LP ba ta gamsu da rawar da Sanata Imasuen ya taka a matsayin shugaban kwamitin ladabtarwa da ɗa'a na majalisa ba kan batun da ya shafi Natasha.
Matasan Najeriya sun caccaki sanatan Edo
Ahanotu ya yi ikirarin cewa an yi amfani da Sanata Imasuen wajen aiwatar da abin da ya kira da tursasawa da wulakanta Sanata Akpoti-Uduaghan ba tare da bincike mai kyau ba.
Idan ba ku manta ba Sanata Natasha ta zargi shugaban Majalisar Dattawa da neman lalata da ita, lamarin da ya tayar da ƙura a Majalisa.
Kennedy Ahanotu ya ce:
"Mu, matasan Najeriya mun yi Allah wadai da matakin da kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ƙarƙashin Sanata Neda Imasuen ya ɗauka kan Natasha wanda ya saɓa wa umarnin kotu.
“Ya bayyana karara ga matasan Najeriya cewa kwamitin bincike da aka tsara zai zauna ranar 11 ga Maris, 2025, an dawo da shi ranar 5 ga Maris, 2025 ba zato ba tsammani, abin tambayar menene na gaggawa?”
Ya ci gaba da cewa hanzarin yanke hukuncin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da kuma halayyar da Sanata Imasuen ya nuna ya ba su mamaki.
An buƙaci yi wa Sanata Neda Imasuen kiranye
Shugaban matasan ya soki yadda Majalisar Dattawa ta 10 ke tafiyar da ayyukanta, yana mai cewa ba ta nuna gaggawa wajen ɗaukar matakai kan batutuwan da suka shafi jin daɗin talakawa ba.
A cewarsa, majalisar ba ta mai da hankali sosai kan gyaran tsarin zaɓe da dokokin da za su inganta harkokin tsaro a ƙasar nan ba.
Bisa haka, Ahanotu ya yi kira da a ɗauki matakan da suka haɗa da, janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha da sake naɗa kwamitin bincike kuma kada a sa Sanata Imasuen.
Ya kuma buƙaci al'ummar mazaɓar Edo ta Kudu su gaggauta fara shirin yi wa Sanata Imasuen kiranye saboda gazawarsa a wakilcin da suka tura shi.
Majalisa ta nemi a cike gurbin sanatoci 2
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta bukaci hukumar INEC ta shirya zaɓukan maye gurbi a mazabun sanatoci biyu.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan bayan ya ayyana kujerun sanatocin a matsayin waɗanda babu kowa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng