Majalisar Ta Ayyana Kujerun Sanatoci 2 a Matsayin babu Kowa a Kansu, Ta Ce INEC Ta Canza Zabe
- Majalisar Dattawa ta tabbatar da kujerun sanatoci biyu a matsayin waɗanda babu kowa a kansu, ta bukaci INEC ta shirya zaɓukan cike gurbi
- Mazaɓun da suka rasa wakilai a Majalisar Dattawa sun haɗa da mazaɓar Sanatan Edo ta Tsakiya da mazaɓar Sanatan Anambra ta Kudu
- A ranar Talata, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya buƙaci INEC ta cike guraben domin al'ummar mazaɓun su samu wakilci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Dattawa ta bukaci Hukumar Zaɓe (INEC) da ta hanzarta gudanar da zaɓen cike gurbi domin maye gurbin kujerun sanatoci biyu da babu kowa.
Majalisar ta aika wannan saƙo ga INEC ne yayin da ta sake tabbatar da kujerun sanatan Edo ta Tsakiya da sanatan Anambra ta Kudu a matsayin babu kowa a kansu.

Asali: Facebook
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a zaman sanatoci na ranar Talata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Ɗan Majalisar da ya jagoranci dakatar da Sanata Natasha ya shiga matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ya na da matuƙar muhimmanci a cike guraben da suka zama babu kowa a majalisar, domin mazabun da abin ya shafa su ci gaba da samun wakilci.
Dalilin da ya sa babu kowa a kujerun sanatoci 2
Kujerar sanatan Edo ta Tsakiya ta zama babu mai rike da ita ne tun a 2024, bayan da Sanata Monday Okpebholo ya lashe zaɓen gwamna a jihar Edo.
An rantsar da shi a matsayin Gwamnan jihar Edo a watan Disamba na 2024, lamarin da ya sa dole sai an maye gurbinsa a majalisa.
Haka nan kuma, kujerar sanatan Anambra ta Kudu ta zama babu kowa a kanta ne tun bayan rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah a watan Yuli na 2024.
Rasuwar sanatan ta haifar da gurbi a majalisar dattawan, wanda har kawo yanzu ba a maye gurbinsa ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Me ya sa INEC ba ta maye guraben ba?
Tun a watan Janairun 2025, INEC ta bayyana cewa tana jiran umarni a hukumance daga Majalisar Dattawa kafin ta shirya zaɓen cike gurbi na Anambra ta Kudu.
Kwamishinar zaɓe a jihar Anambra, Elizabeth Agu, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da cibiyar IPC ta shirya a birnin Awka, babban birnin jihar.
Ta bayyana cewa hukumar zaɓe ba za ta iya gudanar da zaɓen ba har sai ta samu bukatar hakan a hukumance daga majalisar, domin a tabbatar da komai ya tafi dai-dai.
Majalisa ta aika saƙo ga hukumar INEC
Kasancewar wadannan mazabu biyu ba su da wakilai a majalisar dattawa, hakan na iya rage tasirin wakilcin al’ummar yankunan a harkokin siyasa da doka.
Wannan ne ya sa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci INEC da ta hanzarta shirya zaɓen cike gurbi domin mazabun su ci gaba da samun wakilci.
Kotu ta zauna kan shari'ar Akpabio da Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa Godswill Akpabio ya ƙalubalanci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja da cewa ba ta da hurumin sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti ta shigar.
Sanata Natasha ta kai ƙara gaban kotun ne tana ƙalubalantar matakin ladabtarwa da Majalisar Dattawa ta ɗauka a kanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng