El Rufai Ya Girgiza Siyasar Najeriya, Manyan Jiga Jigan APC na Shirin Komawa SDP
- Sauya shekar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP ta fara jawo hankulan manyan ƴan siyasa
- Alamu sun nuna wasu manyan jiga-jigan APC na shirin bin sahun El-Rufai zuwa SDP gabannin babban zaɓen 2027
- Shugaban SDP na ƙasa, Shehu Musa Gabam ya ce jam'iyyar tana da tsare-tsare da manufofin da aka gina ta a kai tun can
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar APC zuwa SDP, akwai alamun cewa wasu manyan ’yan siyasa suna shirin bin sahunsa.
Alamu masu karfi sun nuna cewa wasu manyan jiga-jigan APC da ƴan adawa a ƙasar nan na shirye-shiryen sauya sheka zuwa SDP domin su haɗe da El-Rufai.

Asali: Facebook
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a jiya Litinin a Trust TV.

Kara karanta wannan
2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan matakin da El-Rufai ya dauka ya ja hankalin mutane da dama daga jihar Kaduna, kuma ana sa ran wasu shahararrun jiga-jigan siyasa daga APC da sauran jam’iyyu za su bi sahu.
Waɗanda ake hasashen za su bi El-Rufai
Duk da cewa Gabam bai bayyana sunayen jiga-jigan da za su koma SDP ba, wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun ce ana hasashen har da tsofaffin gwamnoni biyu.
Majiyoyin sun ce tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, na cikin waɗanda shirin sauya sheka zuwa SDP.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da El-Rufai ya yi da Aregbesola da fitaccen limanin cocin nan, Fasto Tunde Bakare, a birnin Lagos a ranar Lahadi.
Haka kuma, El-Rufai ya gana da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a kwanakin baya.
Wadannan tarurruka da ziyarce-ziyarce na El-Rufai sun kara rura wutar jita-jitar cewa ficewarsa daga APC wata alama ce ta sabuwar dabara ta siyasa.
Kayode Fayemi ya musanta barin APC
Duk da haka, Kayode Fayemi, a wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya musanta jita-jitar cewa yana shirin barin APC.
"An jawo hankalina kan wata jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa na raba gari da APC. A baya na sha bayyana cewa ni mamba ne na asali a APC, kuma hakan bai canza ba."
"Ko da yake ina daga cikin masu kira da a yi gyara a cikin jam’iyyar ta hanyar samar da cikakken dimokuradiyya, ina ganin har yanzu ba a makara ba. APC na da damar gyara matsalolinta domin hadin kan ’ya’yanta."
SDP na shirin haɗaka da wata jam'iyya?
A hirar da aka yi da shi, Shugaban SDP, Shehu Musa Gabam, ya jaddada cewa tururuwar da ake yi zuwa SDP wani yunkuri ne na inganta dimokuradiyya a ƙasar nan.
Duk da rade-radin cewa El-Rufai yana da burin takarar shugabancin kasa a 2027, Gabam ya ce jam’iyyar SDP tana da tsare-tsarenta wanda aka gina ta akai.

Asali: Twitter
Shugaban SDP ya ce:
"Manufofin SDP sun fi mayar da hankali kan siyasa tun daga tushe domin tabbatar da cewa duk wani dan takara ya biyo ta hanyoyin da suka dace, maimakon a ba wasu damar mallake jam'iyya.
Ya kuma musanta rade-raɗin cewa SDP za ta yi hadaka da wata jam’iyya, yana mai cewa;
"Ba mu da wani shirin hadaka da wata jam’iyya domin hakan zai haifar da rudani."
APC ta yi magana kan fitar El-Rufai
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta ce fitar El-Rufai daga cikinta zuwa SDP ba za ta hana ta komai ba.
Sakataren APC na reshen jihar Kaduna, Alhaji Yahaya Baba-Pate, ya ce jam’iyyar ba ta damu da ficewar tsohon gwamnan ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng