APC Ta Yi Martani kan Sauya Shekar El Rufai, Ta Fadi Shirin da Take Yi

APC Ta Yi Martani kan Sauya Shekar El Rufai, Ta Fadi Shirin da Take Yi

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta yi martani kan sauya sheƙar da Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi zuwa SDP
  • Sakataren APC a Kaduna, Yahaya Baba-Pate ya bayyana cewa ko kaɗan jam'iyyar ba ta damu da ficewar tsohon gwamnan ba
  • Ya bayyana cewa APC ta maida hankali ne wajen ganin Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani sun sake komawa ofis
  • Sakataren na APC ya yi nuni da cewa a kullum tauraruwar APC na ƙara haskawa a jihar, hakan ya sanya ƴan siyasa ke shigowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta yi magana kan ficewar Nasir Ahmad El-Rufai zuwa SDP.

APC ta bayyana cewa ba ta damu ba kan sauya sheƙar da tsohon gwamnan jihar ya yi zuwa jam'iyyar SDP.

APC ta yi martani kan ficewar El-Rufai
APC ta ce ba ta damu da ficewar El-Rufai ba Hoto: Nasir Elrufai
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa sakataren APC na jihar Kaduna, Alhaji Yahaya Baba-Pate ya bayyana hakan yayin da yake martani kan ficewar El-Rufai.

Kara karanta wannan

'Mutuwa ce kawai za ta raba ni da APC,' Tarihi ya tuna maganganun El Rufa'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

Idan za a iya tunawa, Malam El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga APC zuwa SDP a ranar Litinin, 10 ga watan Maris 2025.

El-Rufai ya bayyana rashin daidaituwar manufofinsa da inda aƙalar APC ta nufa a yanzu, a matsayin babban dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.

Me APC ta ce kan ficewar El-Rufai?

Sai dai, a martanin da ya yi, Alhaji Yahaya Baba-Pate, ya ce jam’iyyar ba ta damu da ficewar tsohon gwamnan ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya bayyana cewa APC ta fi mayar da hankali kan tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaɓen 2027.

Alhaji Yahaya Baba-Pate ya nuna gamsuwa da yadda jam’iyyar ke ƙara ƙarfi a jihar, inda ya ce ƙwararrun ƴan siyasa na ci gaba da shigowa APC a kullum.

"Ba mu damu da sauya sheƙar tsohon gwamna Nasir El-Rufai zuwa wata jam’iyya ba. Babban abin da muke mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani a 2027."

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan Kaduna ya yi magana da El Rufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP

"APC a Kaduna tana ƙara ƙarfi kowace rana, idan muka duba irin manyan ƴan siyasan da ke shigowa cikin jam’iyyar kullum."
"Saboda haka, ba mu damu da wanda ya bar jam’iyya ba, musamman ganin irin tsarin haɗin kan da Uba Sani ya ɓullo da shi."
"Ba mu damu ba, kuma ko a jikinmu saboda El-Rufai ya sauya sheƙa. Jam’iyyar APC a jihar tana ƙaruwa fiye da yadda take a baya."

- Alhaji Yahaya Baba-Pate

Ra'ayin ƴan Najeriya kan sauya sheƙar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan Najeriya sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan sauya sheƙar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi daga APC zuwa jam'iyyar SDP.

Mutane da dama sun nuna farin cikinsu tare da yi masa fatan alheri, yayin da wasu kuma suka caccake shi kan matakin da ya ɗauka na ficewa daga APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng