Datti Baba Ahmed Ya Ce Martabar Musulunci na Raguwa a Mulkin Tinubu
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya ce Musulunci na fuskantar matsala karkashin Bola Tinubu
- A bayanin da ya yi, ya ce addinin Musulunci na fuskantar tabarbarewar martaba a karkashin gwamnatin Tinubu da Kashim Shettima
- An rahoto cewa Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wani taron siyasa da sabuwar jam’iyyar da ya koma ta PRP ta shirya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP, Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa addinin Musulunci na fama da raguwar martaba a karkashin shugabancin Tinubu/Shettima.
An rahoto cewa Datti Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wani taron siyasa da jam’iyyar PRP ta shirya a Abuja ranar Litinin.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Datti Baba-Ahmed ya yi korafi ne duk da cewa shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa suna mulki ne karkashin tikitin Muslim-Muslim.
Matsalar Musulunci karkashin Tinubu
Datti Baba-Ahmed ya kwatanta halin Najeriya da wasu kasashe da shugabanni Musulmi suka jagoranta, yana ambaton misalai kamar Muammar Gaddafi da Saddam Hussein, wadanda ya ce sun sauya rayuwar jama’a.
Baba-Ahmed ya bayyana cewa kalamansa ba wai domin siyasar addini ya yi su ba, sai dai kan shugabanci nagari, yana mai kira da a samar da wakilci na gaskiya ba tare da la’akari da addini ba.
Ya ce:
“Ku saurara da kyau. Ba abu ne mai sauki a gare ni in fadi haka ba. Kuma ina fatan wata rana ba zan yi nadama ba saboda fadin wannan, amma ba abu ne mai sauki ba, amma dole ne a fade shi.”
Baba-Ahmed ya ci gaba da tsokaci kan yadda duniya ke kallon al’amura, yana cewa:
“Duniyar Musulunci ba ta taba fuskantar tabarbarewar martaba kamar yadda take a karkashin shugabancin Tinubu-Shettima ba.
“A duk duniya, inda Musulmi suka yi mulki ko suke yi, akwai zaman lafiya da natsuwa, kuma akwai adalci.”

Source: Twitter
Misalan da Datti Baba Ahmed ya kawo
Yayin da ya yi magana kan shugabannin baya da suka jagoranci kasashe, Datti Baba-Ahmed ya ce sun taka rawar gani wajen kawo sauyi.
Ya ce:
“Ku je kasashen da suka yi shugabanni Musulmi masu zafi... Ina nufin ku fara da Gaddafi. Ku duba Saddam Hussein, duk da take hakkin dan Adam, sun kafa tarihin da har yanzu ba a kai ga irinsa ba.”
Maganar PRP kan sauya shekar 'yan ADC
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana kan yadda ake yawan sauya sheka.
Bayan sauya shekar Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, ya sanar da cewa lokaci ya kusa kurewa 'yan siyasa game da neman takara kuma shi yasa suke sauya jam'iyyu.
Shugaban PRP ya yi magana ne jim kadan bayan karbar Yusuf Datti Baba-Ahmed da ya sauya sheka daga jam'iyyar LP a birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

